Sojojin Nijar ranar Juma'a sun zargi shugaban Majalisar Dinkin Duniya da kin ba su damar shiga Babban Taron Majalisar, suna masu cewa hakan "yana iya kawo cikas a yunkurin kawo karshen rikicin kasarmu".
Sojojin sun kifar da gwamnatin Mohamed Bazoum ranar 26 ga watan Yuli kuma tun daga wancan lokaci suke tsare da shi da iyalansa.
Har yanzu an kasa samun mafita a tattaunawar da ake yi game da halin da kasar ke ciki, inda sojojin suka ce za su mika mulki bayan shekara uku amma kungiyar ECOWAS ta yi kira a yi gaggawar mayar da Bazoum, wanda shi ne zababben shugaban kasa, a kan mulki.
Kasashen duniya da manyan kungiyoyi, ciki har da MDD, sun yi mummunar suka kan masu juyin mulki.
A wata sanarwa da aka karanta a gidan talbijin na kasar, sojojin sun ce Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres "ya kauce hanya wajen gudanar da aikinsa inda ya ki bayar da dama ga Nijar ta halarci Babban Taron MDD karo na 78".
Sanarwar ta caccaki "matakan yaudara" na shugaban MDD, inda ta kara da cewa hakan "yana iya shafar duk wani yunkuri na kawo karshen rikicin kasarmu".
Shugabannin kasashen duniya sun je New York a wannan makon domin halartar Babban Taron Majalisar Dinkin Duniya.
Sojojin sun tura Bakary Yaou Sangare, jakadan Nijar a MDD kafin juyin mulki wanda kuma yanzu shi ne ministan harkokin wajen kasar, domin ya wakilce su a wurin taron.
"Mr Guterres ya ki ambaton sunayen jerin wakilan Nijar a wurin taron... sannan ya amince da bukatar tsohon ministan harkokin waje Hassoumi Massaoudou ta soke mukamin wakilin Nijar na dindindin a Majalisar Dinkin Duniya", a cewar sanarwar sojojin.
Nijar "ta yi tir da babbar murya bisa wannan katsalandan na Mr Guterres a harkokin cikin gida na kasa mai cin gashin kanta," in ji sanarwar.
An tuntubi wakilan Guterres domin yin raddi game da wannan zargi.
Nijar ce kasa ta hudu da aka yi juyin mulki a Yammacin Afirka tun 2020, baya ga Burkina Faso, Guinea da Mali.
Kifar da gwamnatin Bazoum ta jefa fargaba a zukatan kasashen duniya game da zaman lafiyar yankin Sahel, wanda ke fama da hare-haren 'yan ta'adda masu alaka da Al-Qaeda da Islamic State.
Takunkuman da aka sanya wa kasar sun hada da na rufe iyakokin kasashen kungiyar ECOWAS lamarin da ya jefa ta cikin matsanancin karancin abinci da magunguna sannan Nijeriya ta katse lantarkin da take bai wa kasar.
Shugaban Senega Macky Sall ranar Alhamis ya ce har yanzu "akwai yiwuwar" samun mafita ta hanyar diflomasiyya game da rikicin Nijar.
"Ina fata za a yi amfani da hankali wurin samun mafita... har yanzu abu ne mai yiwuwa a samu mafita," in ji Sall a hira da RFI da France 24.