Sojojin da suka yi juyin mulki a Jamhuriyar Nijar sun soke jerin kawancen soji da ke tsakanin kasarsu da Faransa a wani mataki da ake gani zai yi tasiri sosai a yakin da ake yi da masu tayar da kayar baya a yankin Sahel.
Sojojin sun dauki matakin ne ranar Alhamis da daddare a wata sanarwa da suka karanta a gidan talabijin na kasar fiye da mako guda bayan sun kifar da gwamnatin Shugaba Mohamed Bazoum, mutumin da ya amince Faransa ta girke sojojinta a Nijar.
Kazalika sun janye jakadun Jamhuriyar Nijar daga Faransa da Amurka da Nijeriya da kuma Togo.
Hakan na faruwa ne a yayin da wa'adin mako guda da kungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka, ECOWAS ta bai wa sojoji su mika mulki ko su fuskanci fushinta, ciki har da yiwuwar amfani da karfin soji, yake dab da cika.
"Dakarun tsaron Nijar za su mayar da martani mai karfi kuma cikin sauri ga duk wani kutse da za a yi wa Kasar Nijar," in ji sanarwar sojojin.
Sun kara da cewa ba za su bar kowace kasa ta yi musu katsalandan ba "idan ban da kawayenmu da aka dakatar", wato Burkina Faso da Mali, makwabtan Nijar da su ma suke karkashin mulkin soji.
Faransa na da sojoji tsakanin 1,000 zuwa 1,500 wadanda suke taimakawa wurin yaki da 'yan ta'adda da suka addabi yankin Sahel, wadanda ke da dangantaka da al Qaeda da Islamic State.
A shekarar da ta gabata ne Faransa ta janye sojojinta daga Mali sannan ta kai su Nijar bayan dangantaka ta yi tsami tsakaninta da Bamako sakamakon juyin mulkin da sojoji suka yi a kasar.
Mummunan tasiri
Sojojin sun dauki matakin ne a yayin da shi ma zababben Shugaba Mohamed Bazoum a ranar Alhamis ya ce idan juyin mulkin da aka yi masa ya yi nasara, "hakan zai yi mummunan tasiri a kasarmu, da yankinmu da ma duniya baki daya."
A wata makala da ya wallafa a jaridar The Washington Post, Bazoum ya yi kira ga "Amurka da dukkan kasashen duniya su taimaka mana domin dawo da tsarin mulki."
"Sojojin da suka kitsa juyin mulki sun yi karya cewa sun dauki matakin ne domin kare tsaron Nijar. Sun yi zargin cewa yakin da muke yi da 'yan ta'adda masu ikirarin jihadi ya gaza kuma tsare-tsarena na tattalin arziki da walwalar jama'a, ciki har da hada gwiwa da Amura da Turai, suna cutar kasarmu," in ji Bazoum.
Sai dai ya ce ya inganta rayuwar 'yan Nijar da sanya kasar a kan turba mai kyawu.
"A hakikanin gaskiya, tsaron Nijar ya yi matukar inganta — sakamakon hada gwiwar da muke yi wacce sojojin ke adawa da ita. Yanzu tallafin da muke samu daga kasashen waje shi ne kashi 40 na kasafin kudinmu, amma hakan ba zai dore ba idan juyin mulkin ya yi nasara," a cewar Mohamed Bazoum.