Sojojin da suka yi juyin mulki a Jamhuriyar Nijar sun bai wa jakadan Faransa kwana biyu ya fita daga kasar.
Sun bayyana haka ne a wata sanarwa da ministan harkokin wajen kasar ya fitar ranar Juma'a.
Sanarwar ta ce bayan da "jakadan Faransa da ke Yamai ya ki amsa gayyatar" ma'aikatar harkokin waje don yi taro ranar Juma'a da kuma "wasu matakai da Faransa ta dauka da suka ci karo da muradan Nijar", hukumomi sun yanke shawarar soke izinin zaman Sylvain Itte a kasar kuma an ba shi awa 48 ya fita daga cikinta.
Sai dai Faransa ta ce sojojin ba su da ikon korar jakadanta daga kasar.
"Gwamnatin da 'yan Nijar suka zaba ce ta amince jakadan ya yi aiki," kamar yadda ma'aikatar wajen kasar ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP.
Sojojin Nijar sun dauki wannan mataki ne bayan jerin kalamai da zanga-zanga da 'yan kasar suka yi na kyamar Faransa tun bayan juyin mulkin da ya kifar da Shugaba Mohamed Bazoum ranar 26 ga watan Yuli.
Labari mai alaka: Sojojin Nijar sun kama manyan jami'an gwamnatin Bazoum
Sojojin sun zargi Paris da yunkurin yin amfani da karfin soji domin mayar da Bazoum kan mulki kuma sun yi ikirarin cewa Faransa tana amfani da kungiyar ECOWAS domin yi musu barazana.
ECOWAS ta kakaba takunkuman tattalin arziki kan Nijar bayan sojojin sun kifar da gwamnatin Bazoum sannan ta yi barazanar yin amfani da karfin soji domin kawar da su daga mulki.
Faransa ta jibge sojojinta 1,500 a Jamhuriyar Nijar wadanda suke taya kasar yaki da kungiyoyi masu ikirarin jihadi a yankin Sahel.