Hakan na faruwa ne a yayin da wa'adin da sojoji suka bai wa jakadan Faransa a Nijar na fita daga kasar ya wuce./Hoto:AA

Sojojin da suka yi juyin mulki a Jamhuriyar Nijar sun katse wutar lantarki da ruwa na ofishin jakadancin Faransa da ke kasar, sannan sun hana a kai abinci cikinsa, a cewar rahotanni da dama.

Sojojin sun dauki irin wannan mataki a karamin ofishin jakadancin Faransan da ke birnin Zinder, kamar yadda rahotanni suka bayyana ranar Lahadi.

Shugaban kwamitin kasa da ke goyon bayan sojojin mai suna National Support Committee for the National Council for the Safeguarding of the Country (CNSP), Elh Issa Hassoumi Boureima, ya bukaci dukkan hukumomin da ke bayar da ruwa da wutar lantarki da abinci su daina bai wa ofishin jakadancin na Faransa, a cewar rahotanni.

Kazalika, duk hukumar da aka gano tana bai wa ofishin jakadancin Faransa wadannan abubuwa, za a dauke ta a matsayin “makiyiyar al’umma,” in ji rahotanni.

Labari mai alaka: Sojojin Nijar sun kori jakadan Faransa daga kasar

Rahotannin na zuwa ne bayan wa’adin da sojojin suka bai wa jakadan Faransa da ke kasar na awa 48 ya cika ranar Lahadi.

Sojojin na Nijar sun umarci jakadan Faransa Sylvain Itte ya fice daga kasar cikin awa 48 a yayin da ake ci gaba da tayar da jijiyoyin wuya bayan sojoji sun kifar da gwamnatin Mohamed Bazoum a watan jiya.

Nijar ta fada cikin rikici ranar 26 ga watan Yuli bayan Janar Abdourahamane Tiani, wani tsohon shugaban sojojin da ke tsaron fadar shugaban kasar, ya jagoranci kifar da gwamnatin Bazoum.

Bayan nan ne Faransa da wasu kasashen Yamma suka soma kwashe 'ya'yansu daga Nijar.

AA