Sojojin na Nijar sun jima suna yaƙi da ‘yan ta’addan Boko Haram da kuma takwarorinsu na ISWAP a wasu yankunan ƙasar. / Hoto: Forces Armees Nigeriennes

Rundunar Sojin Nijar a ranar Lahadi ta tabbatar da kashe wani babban mamba a ƙungiyar IS da iƙirarin jihadi a wani samame da ƙasar sojojin ƙasar suka kai.

Rundunar ta sanar da cewa dakarunta sun kai samame kan ‘yan ta’addan a ranar Juma’a a yankin Tillaberi a tsakanin iyakokin Niger da Mali da Burkina Faso wadanda ke fama da rikicin ta’addanci.

Sojojin sun bayyana cewa sun kashe Abdoulaye Souleymane Idouwal wanda suka bayyana a matsayin “mai faɗa a ji a ƙungiyar IS”.

Rundunar ta kuma bayyana cewa ta kashe ‘yan ta'adda tara da kuma kama 31 a wani samame da ta kai a yankin a ranar Alhamis.

Sojojin sun yi iƙirarin kassara hanyar sufurin ‘yan ta’addan tare da daƙile hanyoyin sadarwar ‘yan ta’addan.

‘Yan ta’addan na yawan kai wa farar hula hari a yankin na Tillaberi, wanda hakan ke raba mutane da muhallansu.

Nijar na ƙarƙashin mulkin soji waɗanda suka ƙwace mulki a Yulin bara, inda suka ce taɓarɓarewar tsaro na daga cikin dalilan ƙwace mulkin.

Sojojin na Nijar na yaƙi da ‘yan ta’addan Boko Haram da kuma takwarorinsu na ISWAP a wasu yankunan ƙasar.

AFP