Nijar na kuma na fuskantar tashin hankali daga mayakan Boko Haram da kuma abokan hamayyarsu na IS Niger. / Hoto: AFP

An kashe fararen-hula 15 tare da jikkata wasu da dama a wasu hare-haren ta'addanci da aka kai a ƙauyukan yammacin Nijar da ke kusa da iyakar Burkina Faso a farkon makon nan, in ji sanarwar da rundunar sojin ƙasar ta fitar a yammacin jiya Laraba.

"A yankin Mehana, 'yan ta'adda sun kai munanan hare-hare da dama kan fararen-hular da ba su da kariya, inda aka samu mummunar asara," in ji sanarwar, inda aka ce an kashe mutum 14 a wata rana da ba a tantance ba, lamarin da ya biyo bayan mutuwar aƙalla wani farar-hula guda a ranar Talata duk a yanki ɗaya.

Mehana na daga cikin yankuna shida da aka kai hari a yankin Tillaberi na Jamhuriyar Nijar mai iyaka da Mali da Burkina Faso kuma ya zama maɓoyar mayaƙa masu iƙirarin jihadi da ke da alaƙa da kungiyar IS da Al-Qaeda.

Ƙungiyoyin 'yan ta'adda na yawan kai wa fararen hula hari a Mehana, lamarin da ke raba mutane da dama da muhallansu.

Har ila yau, a yankin Tillaberi a ranar Talata, wani farar-hula ɗaya ya mutu, wasu uku kuma suka jikkata, a wani ƙazamin rikici da ya ɓarke tsakanin sashen binciken sojoji da ‘yan ta’adda a kusa da garin Chatoumane, in ji rundunar.

“Jami’an tsaro sun dauki matakin da ya dace, inda suka kashe ‘yan ta’adda da dama,” in ji sojojin.

Kasar Nijar dai na ƙarƙashin jagorancin shugabanin sojoji ne da suka ƙwace mulki a watan Yuli, inda suka ce sun yi hakan ne saboda yadda matsalar tsaro ke ƙara taɓarɓarewa.

Nijar na kuma na fuskantar tashin hankali daga mayaƙan Boko Haram da kuma abokan hamayyarsu na IS da ke yankin yammacin Afirka daga yankin Diffa da ke kudu maso gabashin Nijeriya.

A cewar Acled, wata cibiya mai bin diddigin rikice-rikice, masu iƙirarin jihadi sun kashe fararen-hula da sojoji kusan 1,500 a cikin shekarar da ta gabata a Nijar, idan aka kwatanta da 650 a cikin shekara zuwa Yuli 2023.

AFP