Sojojin Chadi bakwai sun rasu bayan motarsu ta taka nakiya a yankin Tchoukou Telia da ke tafkin Chadi.
Shugaban ƙasar Mahamat Idriss Deby Intno ya ce akwai sojojin ƙasar da dama da suka samu jikkata a lamarin wanda ya faru a ranar Litinin a yankin na Tchoukou mai nisan kilomita 200 daga N’Djamena babban birnin ƙasar.
“Motarsu ta taka nakiya a lokacin da suke sinitiri,” kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito shugaban yana cewa.
Mahamat Itno ya karɓi jagorancin Chadi daga hannun mahaifinsa Idriss Deby Itno wanda ya jagoranci Chadi tsawon sama da shekara 30 kafin ƴan tawaye suka yi sanadin mutuwarsa.
Mista Mahamat a yanzu ɗan takara a zaɓen da za a gudanar 6 ga watan Mayu kuma ba ya fuskantar wani babban ƙalubale sakamakon hukumomin ƙasar sun hana kusan mutum goma takara, daga ciki har da mutum biyu waɗanda suke adawa sosai da gwamnatin sojin ƙasar.
Sojojin Chadi na kashe ko kama masu jihadi akai-akai a yankin tafkin Chadi amma kuma suna fama da asara duk da cewa hakan ya ragu matuka a cikin shekarar da ta gabata.