‘Yan tsirarun jami’an soji da aka sanya aikin gadin ofishin jakadancin Amurka ne kadai suka rage / hoto: AP Archive

An kammala janyewar sojojin Amurka daga Nijar, in ji wani jami'in Amurka a ranar Litinin.

‘Yan tsirarun jami’an soji da aka sanya aikin gadin ofishin jakadancin Amurka ne kadai suka rage, in ji kakakin Pentagon Sabrina Singh ga manema labarai.

A farkon wannan shekarar ne dai gwamnatin Nijar da ke mulkin kasar ta kawo karshen yarjejeniyar da ta bai wa sojojin Amurka damar gudanar da ayyukansu a kasar da ke yammacin Afirka.

Bayan 'yan watanni, jami'ai daga kasashen biyu sun bayyana a wata sanarwar hadin gwiwa cewa sojojin Amurka za su kammala janyewarsu a tsakiyar watan Satumba.

Sansanonin soja na ƙarshe

Amurka ta mika sansanonin soji na karshe a Nijar ga hukumomin kasar a watan da ya gabata, amma kusan sojojin Amurka guda biyu sun rage a Nijar, musamman domin ayyukan gudanarwa da suka shafi janyewar, in ji Singh.

Korar sojojin Amurka da Nijar ta yi bayan juyin mulkin bara na da matukar tasiri ga Washington saboda tilasta wa sojojin yin watsi da muhimman sansanonin da aka yi amfani da su wajen yaki da ta'addanci a yankin Sahel.

Kungiyoyin masu tayar da kayar baya suna gudanar da ayyukansu a yankin da ke kudu da hamadar Sahara.

Daya daga cikin wadannan kungiyoyi, JNIM, tana aiki a Mali, Burkina Faso da Nijar, kuma tana neman fadada zuwa kasashen Benin da Togo.

Sojojin Faransa ma an yi waje da su

An dai yi wa Nijar kallon daya daga cikin kasashe na karshe a yankin da ake fama da tashin hankali da Ƙasashen Yammacin Duniya za su iya hada kai da su domin dakile tashe-tashen hankulan masu tayar da kayar baya.

Amurka da Faransa na da sojoji sama da 2,500 a yankin har zuwa kwanan nan, kuma tare da sauran kasashen Turai sun kashe daruruwan miliyoyin daloli wajen ba da taimako da horar da sojoji.

A 'yan watannin baya-bayan nan Nijar ta janye daga abokan huldar ta na Yammacin Duniya, inda a maimakon haka ta koma kasar Rasha domin neman tsaro.

A cikin watan Afrilu, masu horar da sojoji na Rasha sun isa Nijar don karfafa matakan tsaron sararin samaniyar kasar.

AP