Dakarun rundunar sojin Nijeriya sun kubutar da mutum 13 da aka sace sun kuma kama wasu mutum 11 da ake zarginsu da bai wa ‘yan ta’adda kayayyaki a Jihar Zamfara.
A wata sanarwa da rundunar sojin ta fitar ranar Litinin ta ce dakarun rundunar Hadarin Daji, OPHD da ke aikinta a arewa maso yammacin kasar “a kokarinsu na ci gaba da gudanar da ayyukansu a lokacin rani a yankunan, suna ci gaba da samun nasara.”
“A nasarar da ta samu ta baya-bayan nan, dakarun sun ceto mutum 13 da aka yi garkuwa da su tare da kama wasu 11 da ake zarginsu da samar wa riƙaƙƙun ƴan bindiga kayayyaki a Jihar Zamfara,” a cewar sanarwar, wacce rundunar ta wallafa a shafin X.
Rundunar sojin ta ce an samu nasarar ne a ranar Lahadi 17 ga watan Disamban 2023 a lokacin da dakarun rundunar Hadarin Daji suke wani aiki ne nema da ceto mutane a yankunan Gobirawan Chali da Dangulbi a kusa da Dansadau a ƙaramar hukumar Maru.
“A can ne aka gano mutum 13 din da aka ceto waɗanda ƴan ta’addan suka gudu suka bari a wajen, a ƙoƙarinsu na tserewa a safiyar ranar Lahadin.
“Dukkan mutanen da aka ceto din ƴan ƙauyen Mutunji na garin Dansadau a ƙaramar hukumar Maru ta jihar Zamfara ne, kuma a yanzu suna asibiti ana duba lafiyarsu tare da karɓar bayanai daga gare su.
“Tuni rundunar soji ta miƙa mutanen ga gwamnatin jihar Zamfara don ta sada su da iyalansu.”
Wani samamen
Kazalika, rundunar sojin ta ce dakarun nata sun lalata wata maɓoyar wasu "riƙaƙƙun ƴan ta’adda" a Gidan Jaja da ke ƙaramar hukumar Zurmi a jihar Zamafara.
“Sannan dakarun rundunar OPHD sun kama wasu ƴan ta’adda 11 da ake zarginsu da samar da kayayyaki ga wani riƙaƙƙen ɗan ta’adda Halilu Sububu a Kwanar Boko da ke ƙaramar hukumar zurmi a jihar Zamfara.
“An kama mutanen ne a lokacin da suke ƙoƙarin kai buhun abinci 127 a cikin manyan motoci mallakin Halilu Sububu,” sanarwar ta fada.
Ta ce a yanzu haka ana bincike mutanen don tattara bayanai.
Jihar Zamfara na daga cikin jihohin Nijeriya da ke fama da hare-haren ƴan bindiga a shekarun baya-bayan nan.