Wata rundunar haɗaka ta sojoji da ƴan sandan Nijeriya sun kashe wasu ƴan ƙungiyar IPOB uku a wani ba-ta-kashi da ya faru a yayin wani samame da rundunar ta kai a ranar Litinin da safe, a cewar rundunar sojin ƙasar.
A sanarwar da rundunar sojin ta fitar mai ɗauke da sa hannun daraktan watsa labaranta Birgediya Janar Onyema Nwachukwu, ta ce lamarin ya faru ne a Dajin Igboro da ke tsakanin ƙananan hukumomin Arochukwu da Ohafia da ke Jihar Abiya a kudu maso gabashin ƙasar.
IPOB ƙungiya ce ta ƴan awaren da ke fafutukar kafa ƙasar Biafra a Nijeriya, ƙarƙashin jagorancin Nnamdi Kanu, wanda har yanzu yake tsare sakamakon ƙararsa da gwamnatin ƙasar ke yi bisa tuhumar cin amanar ƙasa.
“Bayan da suka samu nasara a faɗan farko, rundunar ba ta ɓata lokaci ba wajen lalata sansanin da ƴan ƙungiyar ke amfani da su wajen kitsa munanan ayyuka,” in ji sanarwar.
Rundunar sojin ta ce an gano sansanonin ne bayan da aka shafe makonni ana leƙn asiri kan al’amuran IPOB inda aka gano cewa suna amfani da dajin wajen horar da mambobinsu a matsayin sansanin da za su kitsa tare da ƙaddamar da hare-hare a kan fararen hula da jami’an tsaro da cibiyoyin gwamnati a jihar.
Ƙungiyar IPOb ta daɗe tana aiwatar da abubuwa na nuna adawa da gwamnati, ciki har da dokar hana fita duk ranar Litinin da ta taɓa sanya wa a jihohi biyar na Kudu maso Gabashin ƙasar, da nufin tilasta wa gwamnati kan a raba Nijeriya a ba su yankinsu na Biafra.
Sanarwar sojojin ta ƙara da cewa “Bayan lalata sansanin ne dakaru suka gano makamai da harsasai da dama da ma sauran abubuwa.
“Kayayyakin da aka ƙwato sun haɗa da bindigar harba roka shida da motar da ake dora bindiga da AK 47 ɗaya da bama-bamai da rediyon sadarwa irin na jami’an tsaro da kakin soja da sauran su.”
A wani lamarin mai kama da haka, rundunar sojin ta ce a ranar Litinin din kuma dakarunta da haɗin gwiwar ƴan sanda suka dirar wa wani sansani da aka gano ta hanyar bayanan sirri a Ezioha Mgbowo da ke ƙaramar hukumar Awgu a Jihar Enugu.
“Mayaƙan suna kitsa yadda za su tursasa wa mazauna yankin yin dokar zaman gida ne a yayin da dakarun suka dirar musu.
Sai dai an yi nasara a kan mayaƙan, waɗanda suka buɗe wuta a lokacin da suka hangi dakarun tsaro da ke tunkarar sansanin, saboda yadda jami’ai suka mayar da kyakkyawan martani, inda mutum uku daga cikinsu suka mutu sauran kuma suka tsere,” a cewar sanarwar.
A can ma, dakarun sun samu bindigogi da adduna 10 waɗada mayakan suka zubar.
Rundunar sojin te nemi al’ummar yankin da su ci gaba da ba su sahihan bayanai don ƙarfafa yaƙin da suke yi da ta’addanci da sauran munanan anyuka.