Rundunar sojin Nijeriya a ranar Talata ta ce ta kama mutum 19 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban a jihohin Kaduna da Filato.
Rundunar ta ce an kama mutane uku da laifin yin garkuwa da mutane yayin da aka kama hudu da laifin kisan kai.
Haka kuma an kama karin mutum hudu da ake zargi da hannu a kai hare-hare a wasu ƙauyuka, kazalika an kama mutum biyu da laifin safarar miyagun ƙwayoyi yayin da sojojin suka kuma kawar da wasu 'yan fashi hudu.
A wata sanarwa da rundunar ta fitar a shafinta na X, ta ce sojojin sun kuma yi nasarar ƙwato wasu shanu da aka taɓa sacewa a ƙaramar hukumar Mangu ta Jihar Filato.
Sanarwar ta ƙara da cewa: “A ranar 30 ga watan Oktoban 2023, reshen rundunar OPSH ta 7 ya kama wani Alhaji Ya’u Baba da laifin lalata wasu gonaki a kauyen Jagindi Tasha da ke karamar hukumar Jema’a ta jihar Kaduna.
Kazalika, a ranar 2 ga Nuwamban 2023, rundunar ta ce an kama wasu mutane biyu, Edward Dauda da Pam John bisa laifin kai hari kan wani garken shanu da ya kai ga kashe saniya ɗaya a unguwar Sot Gyel da ke karamar hukumar Jos ta Kudu.
Haka kuma, a ranar 2 ga watan Nuwamban 2023, sojojin sun kama wasu shanu 50 da aka sako su kiwo filayen gona a kauyen Kwi da ke karamar hukumar Riyom ta jihar Filato.
“A ranar 1 ga watan Nuwamban 2023, sojoji sun kawar da wasu ‘yan bindiga biyu a kauyen Dutse da ke karamar hukumar Zangon Kataf ta jihar Kaduna.
Hakazalika, a ranar 2 ga Nuwamban 2023, an kuma kawar da wasu 'yan ta'adda biyu, Buwa Tafawa da Gyang Yusuf a kusa da kauyen Tafawa a karamar hukumar Barkin Ladi ta jihar Filato.
A ranar 3 ga watan Nuwamban, a wani aikin hadin gwiwa da sojoji suka yi tare da ‘yan banga an yi nasarar dakile yunkurin kai hari kauyen Kuba da ke karamar hukumar Bokkos ta Jihar Filato da wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba suka yi shirin kaiwa.
An kashe mutum daya daga cikinsu ɓata-garin, yayin da wasu suka tsere da raunukan harbin bindiga.
Sanarwar ta kara da cewa: “A aikin rundunar ‘Operation SAFE HAVEN' na shirin HAKORIN DAMISA IV daga ranar 29 ga Oktoba zuwa 5 ga Nuwamban 2023, an kashe wasu da ake zargi da aikata laifuka.
"Sannan an kama mutum 19 da ake zargi da garkuwa da mutane da kai hare-hare da kuma aikata miyagun laifuka da satar shanu da fashi da makami da kuma lalata gonaki tare da ƙwato wasu makamai da miyagun ƙwayoyi."
A hannu guda kuma an kubutar da wasu mutum hudu daga hannun masu garkuwa da mutane.
Kwamandan Operation SAFE HAVEN, Manjo Janar AE Abubakar, ya jaddada jajircewar shirin OPSH yayin da yake kara ƙarfafa wa al’ummar jihohin Filato da Kudancin Kaduna da kuma Bauchi gwiwa, kan su ci gaba da tallafa wa sojojin wajen ba su hadin kai dakile duk wata ɓarna.
A yanzu haka dai za a gurfanar da mutanen da aka kama a gaban kotu da zarar an kammala bincike.