Wata babbar kotun Saliyo a ranar Laraba ta bai wa tsohon shugaban kasar Ernest Bai Koroma, wanda ake tuhumarsa da laifin cin amanar kasa a wannan wata damar tafiya Nijeriya don a duba lafiyarsa.
Ana tuhumar Koroma mai shekaru 70 da laifuka hudu, ciki har da zargin hannu a yunkurin da sojoji suka yi na hambarar da gwamnatin kasar a watan Nuwamba.
Ana fargaba cewa tuhumar da ake yi wa Koroma na da nasaba da tashin hankali da ya barke bayan zaben kasar na watan Yunin 2023 inda aka sake zaben shugaba Julius Maada Bio a wa'adi na biyu.
Babban dan takarar adawa a zaben ya ki amincewa da sakamakon zaben sannan wasu kasashen waje sun nuna shakku kan sakamakon zaben.
Dakile nasarar juyin mulki
Bayan wasu watanni, a ranar 26 ga watan Nuwamba, wasu ‘yan bindiga sun kai hari a barikin soji da wani gidan yari da kuma wasu yankuna na kasar ta Saliyo, inda suka ‘yantar da fursunoni kusan 2,200 tare da kashe mutane sama da 20.
Bayan haka ne gwamnati ta ce juyin mulki ne da aka yi nasarar dakilewa wanda akasarin masu gadin Koroma suka jagoranta. An gayyaci tsohon shugaban kasar domin amsa tambayoyi a farkon watan Disamba.
Koroma ya yi Allah wadai da harin jim kadan bayan faruwar lamarin, kana lauyoyinsa sun kira tuhumar da ake yi masa da "zargi mara tushe kuma wani bangare na "bangar siyasa".
A ranar Laraba ne alkalin da ke shari'ar ya yanke hukuncin da ya bai wa lauyoyin Koroma nasara kan bukatar neman kotun ta ba shi damar tafiya zuwa kasar waje saboda duba lafiyarsa.
Tafiya zuwa Nijeriya
Za a bar tsohon shugaban kasar ya tafi Nijeriya har na tsawon watanni uku, a cewar alkalin kotun kafin daga bisani ya dage sauraron karar zuwa ranar 6 ga watan Maris.
Kawo yanzu babban alkalin-alkalai na Saliyo ya ki cewa komai kan batun.
A yayin wannan hukunci Koroma bai gurfana a gaban kotu ba a ranar Laraba, a cewar wani wakilin Reuters.
An ba da belinsa ne a lokancin da kotu ta tuhume shi a ranar 3 ga watan Janairu, kuma an tabbatar da cewa ana tsare da shi a gidansa da ke Freetown babban birnin kasar.
A baya Nijeriya ta yi tayin karbar bakoncinsa na wucin gadi, wanda shi kansa ya amince da hakan, a cewar wata wasika daga kungiyar raya tattalin kasashen yammacin Afirka ECOWAS, wadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya gani.
A cewar kundin hukunta manyan laifuka na Saliyo, mutumin da aka samu da laifin cin amanar kasa zai iya fuskantar daurin rai da rai.
Ana kuma tuhumar wasu mutane 12 da laifin cin amanar kasa dangane da juyin mulkin da bai yi nasara ba, ciki har da tsoffin jami'an 'yan sanda da jami'an gidajen gyara hali da kuma wani jami'in tsaro na Koroma.