Shugaban kasar Uganda Yoweri Museveni ya zargi Bankin Duniya da "matsa wa kasarsa" kan batun dokar adawa da auren jinsi da ta yi.
Kalamansa na zuwa ne bayan da a ranar Talata Bankin Duniyar ya sanar da cewa zai dakatar da bai wa kasar, wacce ke Gabashin Afirka sabon bashi saboda dokar da ta sanya ta hana auren jinsi.
Bankin Duniya ya ce dokar ta yi hannun riga da akidunsa kuma daga yanzu ba za a sake gabatar da wani batun bayar da bashi ga shugabannin bankin don neman amincewarsu ba.
Amma Museveni, wanda ya sanya hannu kan dokar hana auren jinsin a watan Mayun da ya wuce, ya wallafa wani sako a shafin Twitter da ke cewa "'Yan Uganda za su samu ci gaba ko an ba su bashi ko ba a ba su ba."
"Don haka abin takaici ne a ce Bankin Duniya da sauran masu ruwa da tsaki suna barazanar tursasa mu yin watsi da imaninmu da al'adunmu da akidunmu da 'yancinmu ta hanyar amfani da kudi," a cewar shugaban kasar.
"Babu wanda ya isa ya matsa mana lamba wajen gaya mana hanyoyin da za mu bi mu warware matsalolin da ke addabar al'ummarmu."
Museveni ya kuma ce Uganda na ci gaba da tattaunawa da Bankin Duniya "ta yadda su da mu duka za mu kauce wa wannan rabuwar hankalin idan zai yiwu."
Ministan Watsa Labarai na Uganda Chris Baryomunsi ya tabbatar wa kamfanin dillancin labarai na AFP a ranar Laraba cewa ana ci gaba da tattaunawa da Bankin Duniyar.
"Sai dai, ya kamata Bankin Duniya da sauran masu ruwa da tsaki su tuna cewa Uganda kasa ce mai cikakken 'yanci da cin gashin kanta, wacce take daukar matakai don muradun al'ummarta kawai."
Uganda na shirin fara hakar danyen man fetur a shekarar 2025 daga yankin yammacin kasar kusa da iyakar Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo, da fatan cewa hakan zai bunkasa tattalin arzikinta da fiye da kashi 7 cikin 100.