80.8% na masu ƙuri'a ne suka fito zaɓen na Oktoba. / Hoto: Reuters

Shugaban Tunisia Kais Saied ya sake lashe zaben kasar da gagarumar nasara a sakamakon da aka sanar ranar Litini, bayan lokacin yakin neman zabe da aka ringa daure abokan hamayyarsa da ‘yan jarida da masu fafutuka da kuma lauyoyi.

Da yammacin Litinin Babbar Hukumar kasar ta Arewacin Afirka kan Harkokin Zabe da aka fi sani da ISIE ta ce Saied ya lashe 90.7% na kuri’un da aka kada – abin da ya nuna cewa magoya bayansa sun kada kuri’a a zaben, yayin da mafi yawan abokan hamayyarsa suka kaurace.

Wanda yake biye masa da yawan kuri’u, dan kasuwa Ayachi Zammel ya samu 7.4% na kuri’un da aka kada bayan zama a gidan kurkuku a mafi yawan lokutan da aka gudanar da yakin neman zabe, inda aka yi masa ɗauri da dama saboda laifukan da suka danganci zabe.

Jami’an zabe sun ce 28.8% na masu zabe ne suka fito, abin da ke nuna mutanen da suka fito ba su kai wadanda suka yi zabe ba a zagaye na farko na zaben kasar da ya gabata.

Zaben shi ne na uku a Tunisia tun bayan boren da aka yi a kasashen Larabawa a 2011, yayin da masu zanga-zanga kan burodi da ‘yanci da kare mutunci suka kai ga hambarar da Shugaba Zine El Abidine Ben Ali.

‘Yan hamayya da aka tsare

A shekarun da suka biyo baya, Tunisia ta kaddamar da sabon kudin tsarin mulki wanda ya kirkiri tsarin jam’iyyu da dama. Sai dai Saied ya fara watsi da sabon kundin tsarin mulkin shekaru biyu bayan ya hau mulki. A watan Yuli na 2021, ya ayyana dokar ta-baci, ya rushe majalsa ya kuma sake rubuta kundin tsarin mulkin kasar don tattara iko a ofishin shugaban kasa.

Awa’adinsa na farko, hukumomi sun ringa dirar wa kungiyoyin fararen hula na kasar, wadanda a baya suke da karsashi.

A shekarar 2023, an kulle wasu daga manyan abokan hamayyarsa na siyasa a kurkuku, har da jagoran masu tsattsauran ra’ayi Abir Moussi da Rached Ghannouchi, mai karfin kishin addinin Musulunci daya daga mutane biyu da suka kafa jam’iyyar Ennahda kuma tsohon shugaban majalisar dokokin Tunisia.

An haramta mutane da dama takara

An kara zafafa kama mutane a farkon bana, lokacin da hukumomi suka fara kama karin lakuyoyi da ‘yan jarida da masu fafatuka kan yin kaura, da tsohon shugaban Hukumar Gaskiya da Mutuntaka da aka kafa bayan zanga-zangar da aka yi

Mutane da dama sun bayyana son tsayawa takarar shugabancin kasa, kuma 17 sun mika takardunsu don neman tsayawa a zaben da aka yi ranar Lahadi. Sai dai mambobin hukumar zaben sun amince da mutum uku ne kawai. Bayan wallafa sunayen na karshe ne kuma, aka kulle Zammel.

Ana sanya alamar tambaya kan matakan da hukumar da shugabanninta su ke dauka a lokacin yakin neman zabe, wadanda dukkansu shugaban kasa ne ya nada su. Sun bijire wa hukunce-hukuncen kotuna da suka umarce su da su mayar da ‘yan takara uku da a baya aka yi watsi da su.

Daga baya majalisa ta zartar da dokar da ta kwace iko daga kotunan.

TRT Afrika