Salva Kiir ne shugaban ƙasar Sundan ta Kudu tun lokacin da ƙasar ta samu ‘yancin kai a watan Yunin shekarar 2011. / Hoto: Reuters

Shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir Mayardit ya kori matamaikan shugaban ƙasa James Wani Igga da Hussein Abdelbagi, tare da shugaban hukumar tsaro ta ƙasa Akech Tong Aleu, a wata dokar da aka karanto a kafar watsa labaran gwamnatın ƙasar.

A wata dokar kuwa, Kiir ya naɗa Benjamin Bol Mel domin ya maye gurbin Wani Igga a a matsayin mataimakin shugaban ƙasa mai wakiltar jam’iyyar SPLM.

Ita kuwa Josephine Lago Yang, shugabar gamayyar jam’iyyu da ƙungiyoyin ‘yan adawa, an naɗa ta ne ta maye gurbin Abdelbagi wanda ya riƙe muƙamin tun shekarar 2020 a ƙarƙashin sharuɗɗan sabuwar yarjejeniyar zaman lafiya.

Kiir ya sake naɗa Wani Igga a matsayin babban sakataren jam’iyyar SPLM mai mulki bayan an cire shi daga matsayin mataimakin shugaban ƙasa.

Shi kuma Charles Chiech Mayor, tsohon matamakin babba daraktan hukumar tsaro ta ƙasa, an naɗa shi muƙaddashi ne babban daraktan hukumar.

An kori Akech Tong Aleu ne daga aiki bayan ya yi wata huɗu a muƙamin, Ba a bayyana dalilin cire manyan jami’an gwamnatin ba.

Sudan ta Kudu tana ɗaya daga cikin ƙasashe kaɗan da ke da mataimakan shugaban ƙasa biyar, wani tsarin da aka kafa a ƙarƙashin yajejeniyar zaman lafiyar 2018.

TRT Afrika