Habasha ta ce ta yi wa Shugaba Mohamoud "kyakkyawar tarba" tare da nuna masa girmamawa irin wadda aka bai wa dukkan shugabannin ƙasashen da suka halarci taron./Hoto: TRT World

Shugaban Somalia Hassan Sheikh Mohamoud ya zargi jami'an tsaron Habasha da yunƙurin hana shi shiga zauren taron Ƙungiyar Tarayyar Afirka da ake yi a Addis Ababa, inda hukumomin Mogadishu suka bayyana matakin a matsayin "taƙalar faɗa".

Shugaba Mohamoud ya yi zargin ne ranar Asabar a yayin da ake ci gaba da samun takun-saƙa tsakanin Addis Ababa da Mogadishu game da yarjejeniyar da Ethiopia ta ƙulla da yankin Somaliland wanda ya ɓalle daga Somalia a kan ba da damar amfani da tashar jiragen ruwa .

"A wannan safiya lokacin da na shirya domin zuwa wurin rufe taron, jami'an tsaron Habasha sun toshe hanyata," a cewar Mohamoud a hira da manema labarai a Addis Ababa, bayan daga bisani an ba shi hanyar shiga wurin taron.

Ya ce shi da shugaban ƙasar Djibouti Ismail Omar Guelleh sun sake gwada yunƙurin shiga wurin taron, amma aka hana su.

"Wani soja riƙe da bindiga ya tsaya a kusa da mu inda ya hana mu shiga wurin," in ji shi.

Sai dai a martanin da ta yi nan-take, Habasha ta ce ta yi wa Shugaba Mohamoud "kyakkyawar tarba" tare da nuna masa girmamawa irin wadda aka bai wa dukkan shugabannin ƙasashen da suka halarci taron.

Billene Seyoum, mai magana da yawun Firaiministan Habasha Abiy Ahmed ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa an dakatar da tawagar Somalia daga shiga wurin taron yayin da jami'an tsaron ƙasar suka yi yunƙurin shiga wurin ɗauke da makamai.

"Jami'an tsaron Somalia sun yi yunƙurin shiga wurin taron AU ɗauke da makamai abin da ya sa jami'an tsaron AUC suka dakatar da su," a cewarta.

Ma'aikatar harkokin wajen Somalia ta fitar da sanarwa da ke yin tir da "taƙalar faɗa da gwamnatin Habasha ke yi ta hanyar yunƙurin hana tawagarmu shiga wurin taron".

Ta yi kira ga ƙungiyar AU ta gudanar da "ƙwaƙƙwara kuma sahihin bincike game da wannan mugun nufi".

TRT Afrika da abokan hulda