Tun a ranar 15 ga watan Afrilu aka soma rikici tsakanin sojin Sudan da RSF. Hoto/Reuters

Shugaban sojojin Sudan Janar Abdel Fattah Al Burhan, ya zargi takwaransa na RSF da aikata laifukan yaki, a daidai lokacin da rikicin kasar ke kara kazanta.

Sudan na fuskantar “ta’addanci” mafi muni a tarihi, kamar yadda Al Burhan ya bayyana a wani jawabi da ya yi ta talabijin inda yake tunawa da cikar rundunar sojin Sudan shekara 69 da kafuwa.

Kasar na fuskantar “makirci mafi girma a tarihinta, inda yake tasiri kan mutane da kabilunsu da asalinsu.

Kasar tana fuskantar ''makirci mafi girma a tarihinta na zamani, wanda aka far wa muhalli da asali da gado da makomar al'ummarmu, wadanda suka kasance tun safiyar ranar 15 ga Afrilu, suke fuskantar ta’addanci da yaki mafi girma a hannun maciya amanar kasa Hemedti da makarrabansa,” in ji Al Burhan.

Babu wani martani nan take daga sojojin Hemdeti na RSF kan wannan zargin. Rikicin da ake ci gaba da yi a Sudan ya yi sanadin mutuwar sama da mutum 3,000 da kuma raba sama da mutum miliyan uku da muhallansu.

Majalisar Dinkin Duniya ta zargi duka bangarorin da laifukan yaki, inda Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya take bincike.

Hamdan Dagalo wanda aka fi sani da Hemedti, shi ne mataimakin Al Burhan a gwamnatin rikon kwarya ta sojin kasar bayan sun yi juyin mulki a 2021.

Mutanen biyu sun raba gari a farkon shekarar nan sakamakon rashin jituwa a tsakaninsu.

Rashin jituwar asali kan batun mayar da rundunar RSF karkashin sojin kasar ne.

Al Burhan ya yi amfani da ranar soji ta kasar domin gode wa “makwafta da abokai” wadanda suke son kawo karshen wannan rikici.

“Za mu ci gaba da zama ƙwararrun dakaru da suke tare da ra’ayoyin jama’a da kuma kuma dokar kasa, dimokuradiyya da cibiyoyi,” kamar yadda ya kara da cewa.

TRT Afrika