Shugaban Sojin Sudan Abdel Fattah al-Burhan ya kai ziyara sansanin sojin ruwa na Flamingo a Sudan. Hoto/AFP

Shugaban sojin Sudan Abdel Fattah al-Burhan ya tafi Masar a ranar Talata, a karon farko da ya tafi wata kasa tun bayan da aka soma yaki tsakanin sojojin kasar da rundunar RSF a watan Afrilu.

Ana sa ran Janar Burhan zai tattauna da Shugaban Masar Abdel Fattah al-Sisi “kan ci-gaba na baya-bayan nan na Sudan da kuma batun dangantaka tsakanin kasashen biyu”, kamar yadda majalisar sojin ta bayyana a wata sanarwa.

Sudan ta fada cikin rikici a tsakiyar Afrilu bayan rundunar RSF karkashin jagorancin Mohammed Hamdan Dagalo da kuma rundunar sojin kasar karkashin al-Burhan suka soma rikici da juna.

Wannan rikicin ya mayar da babban birnin kasar Khartoum fagen daga inda RSF ke da iko da yankin mai dumbin yawa na birnin.

Sansanin sojin da ake zargin al-Burhan yake tun bayan soma wannan rikicin a watan Afrilu na daga cikin yankunan birnin da rikicin ya fi kamari.

Dangantaka mai tsohon tarihi

Burhan ya yi kokarin barin hedikwatar sojin kasar a makon jiyya, inda a nan ne yake zama tun bayan da rikicin ya barke. Ya kai ziyara zuwa wasu sansanonin sojin da ke Omdurman da wasu sassa na kasar.

Burhan ya yi tafiya zuwa Masar daga birnin Port Sudan da ke gefen Bahar Maliya. Duk da watannin da aka shafe ana rikici, babu bangaren da ya samu cikakken iko da babban birnin kasar Khartoum, ko sauran muhimman wurare a kasar.

A makon da ya gabata, an ga hayaki ya turnuke sararin samaniyar birnin a wasu muhimman wurare da ke kusa da filin jirigin birnin.

Masar na da tsohuwar dangantaka da sojojin Sudan da manyan janarorinta. A watan Yuli, Janar al-sisi ya karbi bakuncin makwaftan Sudan inda ya sanar da tsagaita wuta.

An yi yarjejeniyar tsagaita wuta wadda ba ta dore ba inda aka yi ta Amurka.

Reuters