Shugaban Senegal Macky Sall ya kare matakinsa na ɗaga zaɓen ƙasar bayan zanga-zangar da ta ɓarke a ƙasar a ranar Juma’a a ƙasar.
A wata tattaunawa da aka yi da shi a karon farko bayan ɗaga zaɓen, Sall ya yi watsi da zarge-zargen da ake yi kan cewa matakin da ya ɗauka ya saɓa wa shari’a.
Ya bayyana cewa ƙasar na buƙatar ƙarin lokaci domin magance matsalolin da take fuskanta kan cire sunayen wasu ƴan takara saboda rashin cancanta da kuma rikicin da ake yi tsakanin ɓangaren majalisa da kuma na shari’a.
Senegal na daga cikin ƙasashen Yammacin Afirka da ke da dimokuradiyya wadda ke tsaye da gindinta, sai dai a halin yanzu dimokuradiyyar ƙasar na cikin barazana tun bayan sanarwar ɗaga zaɓen.
Zanga-zanga
Macky Sall ya musanta cewa yana so ya ci gaba da mulki a ƙasar. “Babu abin da nake nema baya ga na bar ƙasar cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali,” kamar yadda Sall ya bayyana.
“ A shirye nake na miƙa mulki. A shirye nake da hakan a kullum.” Sall ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AP cewa a cikin fadar shugaban ƙasar da ke Dakar, a lokacn da yake waje, ɗaruruwan mutane sun fito kan tituna inda suke ƙona tayoyi da jefa duwatsu.
Aƙalla ɗalibi ɗaya aka kashe a makaranta bayan da aka yi zanga-zanga a birnin Saint Louis da ke arewacin kasar, kamar yadda wata sanarwa daga mai shigar da ƙara na ƙasar ta bayyana.
“Makomarmu na cikin wani hali,” in ji Mohamed Sene, mai shigar da ƙara a Dakar.
Sall wanda ya hau kan karagar mulki a shekara ta 2012 kuma yana shirin kammala wa'adinsa na biyu a ranar 2 ga watan Afrilu, inda ya dage zaben da aka shirya yi a ranar 25 ga watan Fabrairu a daidai lokacin da ake shirin fara yakin neman zabe.