An tsara gudanar da zaɓen a ranar 25 ga watan Fabrairu. / Hoto: Reuters

Shugaban ƙasar Senegal Macky Sall ya ce wa'adin mulkinsa zai ƙare ranar 2 ga watan Afrilu kamar yadda dokoki suna tanada, amma bai bayyana ranar gudanar da zaɓen shugaban ƙasar da ya ɗage a farkon wannan wata ba.

Sall ya fuskanci gagarumar suka daga ciki da wajen ƙasar tare da jerin zanga-zanga bayan da haka kwatsam ya ɗage zaɓen shugaban ƙasar da ya kamata a gudanar ranar 25 ga watan Fabrairu zuwa watan Disamba.

Sukar da yake sha da kuma hukuncin da Kotun Tsarin Mulkin ƙasar ta yanke cewa ɗage zaɓen ya saɓa wa doka ne ska sa ya gabatar da jawabi ga ƴan ƙasar ranar Alhamis.

A jawabin nasa, Shugaba Salla ya ce ba zai sanya sabuwar ranar gudanar da zaɓe ba sai an kammala wani taron sulhu na siyasa da za a soma a ƙasar ranar Litinin mai zuwa.

"Wa'adin mulkina a matsayin shugaban ƙasar Senegal zai ƙare ranar 2 ga watan Afrilu, 2024," in ji Shugaba Sall, bayan da ƴan ƙasar suka riƙa raɗe-raɗin cewa yana so ya tsawaita wa'adin mulkinsa.

Ya ƙara da cewa: "Amma game da ranar gudanar da zaɓen, za mu ga yadda za ta kaya a yayin da za a yi taron sulhu. Za a iya gudanar da zaɓen kafin ko bayan ranar 2 ga watan Afrilu."

A wani mataki da ake gani a matsayin yunƙurin rarrashin ƴan ƙasar, Shugaba Sall ya ce yana duba yiwuwar sakin manyan ƴan adawa biyu Ousmane Sonko da Bassirou Diomaye Faye.

TRT Afrika da abokan hulda