Janar Abdourahamane Tchiani ya karbi mulki ne a watan Agustan 2023 bayan juyin mulkin da aka yi wa shugaban Nijar Mohamed Bazoum. / Hoto: Ofishin Shugaban Jamhuriyar Nijar

Shugaban mulkin sojan Nijar Janar Abdourahamane Tiani ya tattauna ta wayar tarho a ranar Talata da shugaban ƙasar Rasha Vladimir Putin game da "ƙarfafa haɗin gwiwar tsaro", a cewar sanarwar da aka fitar a hukumance.

Tuni dai ƙasashen biyu suka amince a watan Janairu domin ƙarfafa alaƙar soji a lokacin da Firaministan Nijar Ali Lamine Zeine ya jagoranci wata tawaga zuwa birnin Moscow.

Nijar ta kasance kan gaba a haɗin gwiwa da Ƙasashen Yammacin Duniya wajen yaƙar masu tayar da ƙayar-baya a yankin Sahel, amma ta rungumi Rasha a matsayin sabuwar abokiyar tsaro tun bayan hamɓarar da zaɓaɓɓen shugaban ƙasar a bara.

Shugabanin ƙasashen biyu "sun yi magana kan buƙatar ƙarfafa haɗin gwiwa a fannin tsaro...domin shawo kan barazanar da ake fuskanta a halin yanzu," in ji sanarwar ta Nijar, wadda aka karanta a gidan rediyon gwamnatin ƙasar.

'Dabarun haɗin kai'

Har ila yau, sun tattauna "ayyukan don haɗin gwiwar ɓangarori da dama da na duniya," in ji sanarwar, ba tare da ba da ƙarin bayani ba kan hakan.

Janar Tiani, wanda ya jagoranci Nijar tun bayan juyin mulkin watan Yuli, ya gode wa Putin saboda "goyon bayan" da Rasha ke ba ƙasar ta yankin Sahel da kuma gwagwarmayar neman ƴancin kan ƙasa.

Tawagar Rasha ma ta ziyarci Nijar a watan Disambar da ya gabata.

Har yanzu dai dakarun Amurka kusan 1,000 na jibge a Nijar duk da cewa an taƙaita zirga-zirgarsu tun bayan juyin mulkin, kuma Washington ta daƙile tallafin da take bai wa gwamnatin.

Nijar ta ayyana daina alaƙar soji da Ƙasashen Yamma

Wata babbar tawagar Amurka ta je Yamai a tsakiyar watan Maris domin sabunta hulɗa da gwamnatin mulkin soja, amma ta ce ba su gana da Tiani ba.

Sabuwar gwamnatin ta yi Allah wadai da haɗin gwiwar soji da Ƙasashen Yamma, tare da yin watsi da alaƙar mulkin mallaka da Faransa.

A baya dai Nijar ta kasance muhimmin sansani ga ƙoƙarin sojojin Faransa na murƙushe ta'addancin da ya samo asali daga yankin Sahel.

Nijar ta bi sahun ƙasashen maƙwabta Mali da Burkina Faso a farkon wannan wata wajen sanar da kafa rundunar haɗin gwiwa da za ta yaƙi hare-haren ta'addancin da aka daɗe ana fama da su a cikin ƙasashen uku.

A watan Janairu ne dai suka bayyana aniyarsu ta ficewa daga ƙungiyar ECOWAS ta ƙasashen yankin Yammacin Afirka.

TRT Afrika da abokan hulda