Shugaba Emmanuel Macron ya shaida wa shugaban Senegal mai jiran gado Bassirou Diomaye Faye cewa Faransa tana so ta "ci gaba da dangantakarar da ke tsakanin kasashen biyu."
Ofishin shugaban ƙasar Faransa ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma'a.
Macron ya taya Faye "murna" a kan nasarar da ya samu a zaɓen shugaban ƙasar da aka gudanar ranar Lahadin da ta gabata, musamman yadda aka gudanar da shi ba tare da wata matsala ba, yana mai jinjina wa "ƴan ƙasar Senegal bisa zaɓen" abin da suke so", in ji ofishinsa.
A tattaunawarsu ta farko ta wayar tarho tun bayan kammala zaɓen, Macron da Faye sun tattauna kan "ƙulla dangantaka a tsakaninsu tare da halin da ake ciki a yankin," a cewar fadar shugaban Faransa mai suna the Elysee Palace.
An saki Faye, mai shekara 44, daga kurkuku kwanaki 10 kafin zaɓen da aka gudanar ranar 24 ga watan nan na Maris inda ya doke Amadou Ba, ɗan takarar gamayyar jam'iyyu masu mulki.
Aminiya
Babban ubangidansa a siyasa Ousmane Sonko ya sha caccakar Faransa, ƙasar da ta yi wa Senegal mulkin mallaka, sai dai bayan Faye ya lashe zaɓen ya ce Senegal za ta ci gaba da zama aminiyar dukkan ƙasashen waje da ke ƙawance da ita.
Faransa ta yi maraba da wannan kalamai musamman ganin cewa tasirinta na raguwa a ƙasashen Yammacin Afirka da ta yi wa mulkin mallaka.