Shugaban kasar Chadi Janar Mahamat Idriss Déby Itno ya tattauna da manyan masu ruwa da tsaki kan harkokin kasar Nijar a yayin da kungiyar ECOWAS ta yi barazanar daukar mataki kan sojojin kasar idan ba su mayar da Mohamed Bazoum kan mulki ba nan da mako daya.
Shugabannin kungiyar ta ECOWAS ne suka aiki Janar Déby domin yin sulhu kan rikicin kasar ta Nijar a daidai lokacin da sojoji suke ci gaba da tsare Shugaba Bazoum.
Sojojin da ke tsaron fadar shugaban kasar ne suka kifar da gwamnatin Bazoum sannan suka kafa Majalisar Kare Kasa mai suna National Council for the Safeguarding of the Fatherland (CNSP) a turance wadda Janar Abdourahamane Tchiani yake jagoranta.
Wata sanarwa da shugaban Chadi ya wallafa a shafinsa na Twitter ranar Litinin ta ce ya yi ganawa daban-daban da sojojin da suka yi juyin mulki da Shugaba Bazoum da kuma tsohon shugaban kasar Mahamadou Issoufou wanda ke da matukar tasiri a siyasar Nijar.
''Na yi ganawa mai zurfi da shugabannin National Council for the Safeguarding of the Fatherland (CNSP), musamman Janar Abdourahamane Tchiani, da Shugaba Mohamed Bazoum da kuma tsohon Shugaba Mahamadou Issoufou,'' in ji Mahamat Deby.
Tattaunawar na son "lalubo dukkan hanyoyin da suka kamata a bi don warware rikicin da ke addabar makwabciyarmu (Nijar) cikin lumana,'' a cewarsa.
Sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar sun gargadi kasashen waje kan su guji tsoma baki a sha'anin cikin gida na kasar domin gudun abin da ka iya biyo baya.