Janar Abdel Fattah al-Burhan, jagoran gwamnatin rikon kwaryar Sudan, ya sauke wasu ministocinsa ciki har da ministan harkokin waje da kuma ya nada wasu sabbi a ranar Lahadi.
A wata sanarwa, majalisar koli ta sojin Sudan ta ce Janar al-Burhan ya sallami Ministan Harkokin Wajen Kasar Hussein Awad Ali kuma ya maye gurbinsa da Ali Youssef Ahmed a matsayin ministan harkokin waje na riko.
Kuma an maye gurbin ministan yada labarai Graham Abdelkader da Khalid Ali Aleisir.
Kazalika Omar Bakhit ya maye gurbin Ministan Harkokin Addinai Osama Hassan Mohamed Ahmed.
Garambawul din ya zo ne daidai lokacin da ake ci gaba da samun rikici tsakanin rundunar sojin Sudan da dakarun RSF, abin da ya yi sanadin mutuwar fiye da mutum 20,000 kuma ya yi sanadin raba mutum miliyan 10 da muhallinsu tun bayan fara yakin a watan Afrilun shekarar 2023, kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana.
Kasashen duniya da Majalisar Dinkin Duniya suna ci gaba kara yin kira da a kawo karshen rikicin, yayin da yakin yake ci gaba da barazanar jefa ƙarin miliyoyin mutane cikin matsananciyar yunwa saboda ƙarancin abinci a jihohi 13 cikin 18 na ƙasar.