Shugaban Ƙasar Kamaru mai shekaru 91, Paul Biya, na cikin ƙoshin lafiya, in ji gwamnati a ranar Talata, inda sanarwar da aka fitar ta kira rahotannin da ake yaɗawa cewa ba shi da lafiya da sunan "tsagwaron shaci-faɗi".
Ba a sake ganin Biya a bainar jama'a ba tun bayan halartar taron China-Afirka a Beijing a watan Satumba.
Gazawarsa ta halartar taron da aka shirya a Faransa a makon da ya gabata ya sanya fargabar cewa tsohon ba shi da lafiya.
"An yi ta yada jita-jita a kafafen sadarwa game da yanayin lafiyar shugaban," in ji sanarwar da kakakin gwamnati Rene Sadi ya fitar.
Ana ta kiraye-kiraye game da inda Biya ya shiga
"Gwamnati na bayyana cewar waɗannan jita-jita da shaci-faɗi ne kawai ...kuma tana musanta waɗannan rahotanni da ake yaɗawa."
Jam'iyyun adawa da ƙungiyoyin farar-hula na ta yin kira a bayar da bayanai game da yanayin lafiyar Biya da kuma inda yake.
Bayan taron Beijing, Biya ya ziyarci wani asibiti mai zaman kansa a Turai, in ji Sadi. "Shugaban Ƙasa na cikin ƙoshin lafiya kuma zai dawo Kamaru nan da 'yan kwanaki."
Ta yadda babu wani shiri na wa zai gaji Biya, rashin ganinsa zai kawo rashin tabbas ɗin siyasa a Kamaru.
Kamaru da ke fitar da albarkatun koko da man fetur, wadda kuma ta yi shugabannin ƙasa biyu kawai tun bayan samun 'yanci daga hannun Turawan mulkin-mallaka na Faransa da Birtaniya a farkon 1960, na cikin rikicin 'yan a-ware da suka kashe dubban mutane da rikicin Boko Haram a arewacin ƙasar.