Shugaban Access Bank Herbert Wigwe da matarsa da ɗansa da kuma wasu mutane sun rasu sakamakon hatsarin jirgin sama a jihar California da ke Amurka, kamar yadda hukumomi suka tabbatar.
Sun rasu ne ranar Asabar da safe a agogon Nijeriya a yayin da jirginsu yake kan hanyar zuwa birnin Las Vegas.
Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen saman Amurka ta ce ta soma bincike kan musabbabin hatsarin.
Ta ce mutum shida ne a cikin jirgin kuma dukkansu ba su tsira ba.
Tsohon shugaban kasuwar hada-hadar hannayen-jari ta Nigerian Exchange Group Abimbola Ogunbanjo na cikin waɗanda suka rasu.
Tsohuwar Ministar Kuɗi ta Nijeriya kuma shugabar Hukumar Cinikayya ta Duniya Ngozi Okonjo-Iweala ta tabbatar da rasuwar Wigwe da sauran mutanen a saƙon da ta wallafa a shafinta na X.
“Na yi matuƙar girgiza da samun labarin mutuwar Herbert Wigwe da matarsa da ɗansa da kuma Bimbo Ogunbanjo a hatsarin jirgin helikwafta,” in ji Okonjo-Iweala.
Ana kallon Wigwe, mai shekara 57, a matsayin ɗaya daga cikin mutanen da suka kawo gagarumin sauyi a tsarin bankunan Nijeriya, inda ya taɓa yin aiki a Guaranty Trust Bank a matsayin darakta kafin ya tafi Access Bank.
Mutuwarsa “babban koma-baya ne” ga fannin bankin Nijeriya da na Afirka, a cewar kakakin shugaban Nijeriya Bayo Onanuga a saƙon da ya wallafa a shafin X.