Shugaba Tinubu ya bayar da umarni a gudanar da bincike kan kisan sojoji shida a Borno

Shugaba Tinubu ya bayar da umarni a gudanar da bincike kan kisan sojoji shida a Borno

Wannan na zuwa ne bayan 'yan ta'addan ISWAP sun kai hari wani sansanin soji da ke Sabon Gida a Ƙaramar Hukumar Damboa.
Hedkwatar Tsaron Nijeriya a ranar Laraba ta ce mambobin ƙungiyar ta’addanci ta ISWAP ne suka kai kai hari da Asuba a sansanin sojin. / Hoto: Fadar Shugaban Nijeriya

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya jajanta wa sojojin ƙasar dangane da sojojin da aka kashe yayin wani hari da aka kai wani sansanin soji da ke Sabon Gida a Ƙaramar Hukumar Damboa ta Jihar Borno.

Mai magana da yawun shugaban ƙasar Bayo Onanuga ne ya tabbatar da hakan a ranar Alhamis inda ya ce shugaban ya buƙaci da gudanar da bincike mai zurfi kan yadda lamarin ya faru domin guje wa afkuwar irin hakan a nan gaba.

Hedkwatar Tsaron Nijeriya a ranar Laraba ta ce mambobin ƙungiyar ta’addanci ta ISWAP ne suka kai kai hari da Asuba a sansanin sojin.

Hedkwatar ta ce ‘yan bindigan sun kai harin ne a kan babura a sansanin da ke Sabon Gari.

“Wannan matakin da rundunar ta dauka ya nuna iyawa da kuma shirye-shiryen sojojin mu na tunkarar matsalolin da ke barazana ga tsaron kasarmu. Ayyukan da suka yi ya shaida kudurinmu na kawar da ta’addanci da ‘yan fashi da makami, tare da share fagen samar da zaman lafiya da tsaro ga daukacin ‘yan Nijeriya,” in ji Shugaban.

“Ina mika godiya da kuma jaje ga sojojinmu da jami’an tsaro a madadin ƙasa baki ɗaya.

"Ba za a manta da sadaukarwarku da jajircewarku ba, kuma tare da kuma ɗari bisa ɗari a wannan yaƙin domin kawar da wannan barazanar."

TRT Afrika