Shugaban kasar Kamaru Paul Biya ya sauka a babban filin jiragen sama na Yaounde a ranar Litinin, bayan da ya shafe makwanni da barin kasar, inda aka yi ta jita-jita game da lafiyarsa, kamar yadda gidan talabijin na kasar CRTV ya nuna.
An nuna shugaban kasar mai shekara 91 a gidan talabijin a lokacin da yake sauka daga jirgi, inda ya dinga musabaha da jami'an da ke kusa da matarsa Chantal, a daidai lokacin da jama'a ke ta murna suna jiran tarbarsa.
Magoya bayansa da suke jeru a titi sun yi ta buga ganguna da rera waƙoƙi ɗauke da hotunansa, a lokacin da shugaban ke wucewa don tafiya fadarsa, kamar yadda kafar yada labarai ta CRTV ta bayyana, a yayin da take watsa yadda saukar tasa ta kasance.
An yi ta kokwanto kan halin lafiyar Biya da kuma inda ya tafi bayan da aka daina jin ɗuriyarsa tun bayan taron da ya halarta na ƙasashen Afirka da China a birnin Beijing a watan Satumba.
'Jita-jita ta ƙare'
Mai gabatar da shirye-shirye a gidan talabijin na CRTV ya ce "A yau shugaban kasa na kan hanyarsa ta dawowa, kuma hakan zai kawo ƙarshen jita-jitar da ake yaɗawa."
Shafin da ke bin diddigin zirga-zirgar jiragen sama ya nuna jirgi ƙirar Boeing mai lamba CMR001, wanda shi ne Biya ke hawa, ya bar birnin Geneva na Switzerland a ranar Litinin, inda a can shugaban yake tsawon makonni, in ji majiyoyin hukuma.
An mammanna manyan fastocin shugaban ƙasar wanda ya shafe shekara 40 yana mulki ba hamayya a babban birnin kasar ana yi masa maraba gabanin komawar tasa.
Wani wakilin kamfanin dillancin labarai na AFP da ke wajen ya ce an rubuta a ɗaya daga cikin allunan cewa "Barka da dawowa gida, Shugaban Kasa."
Haramta wa kafafen yada labarai magana
A ranar 8 ga watan Oktoba ne gwamnatin ƙasar ta fitar da sanarwa bayan da aka yi ta yaɗa jita-jita, inda ta ce Shugaban Ƙasar ya kusa komawa gida.
Sannan a hukumance gwamnati ta haramta wa kafafen yada labarai na cikin gida tattaunawa kan yanayin lafiyarsa.
Har ila yau shugaban na Kamaru bai halarci babban taron Majalisar Dinkin Duniya da aka gudanar a birnin New York ba, da kuma taron kasashe masu magana da harshen Faransanci a birnin Paris.