Shugaban Ghana John Dramani Mahama ya bayar da umarnin soke duk wani fasfo na diflomasiyya da kuma na aiki wanda gwamnatin baya ta Nana Akufo-Addo ta bayar.
Dakta Callistus Mahama, wanda shi ne babban sakatare ga shugaban ƙasar ne ya sanar da hakan a wata wasiƙa da ya aika ga daraktan ma’aikatar harkokin waje na ƙasar, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Ghana ya ruwaito.
Wasiƙar ta yi ƙarin haske inda ta ce gwamnatin Shugaba Mahama ta ɗauki wannan matakin ne domin tabbatar da an yi amfani da takardun tafiye-tafiye na gwamnati yadda ya kamata da kuma bin tsarin ƙasa da ƙasa.
Haka kuma wasiƙar ta buƙaci ma’aikatar ta ɗauki mataki domin aiwatar da sabon umarnin.
Daga cikin matakan da za ta ɗauka har da sanar da duk masu ɗauke da fasfo din game da matakin da kuma mayar da su ga ma’aikatar domin sake ba su sabo idan har da yiwuwar hakan.
A ranar 7 ga watan Janairu ne aka rantsar da sabon shugaban ƙasar na Ghana John Dramani Mahama bayan ya lashe zaɓen ƙasar wanda aka gudanar 7 ga watan Disamabar 2024.
Mahama ya maye gurbin Nana Akufo-Addo, wanda ya sauka bayan kammala wa'adi biyu na shugabanci.