Shugaban Ghana John Dramani Mahama ya miƙa sunayen rukunin farko na ministoci ga kakakin majalisar ƙasar domin amincewa.
Shugaban ya yi haka ne domin biyayya ga sashe na 78 na kundin tsarin mulkin Ghana na shekarar 1992.
Daga cikin waɗanda Shugaba Mahama ya naɗa a matsayin ministoci akwai Dakta Cassiek Ato Baah Forson a matsayin Ministan Kuɗi, da Mista John Abdulai Jinapor a matsayin Ministan Makamashi, da Dakta Dominic Akuritinga Ayini a matsayin Antoni Janar kuma Ministan Shari’a.
Dakta Cassiel Ato Baah Forson
Dakta Cassiel Ato Baah Forson masanin tattalin arziƙi ne kuma ƙwararran akanta ne, haka kuma masanin harkokin haraji tare da ƙwarewa kan sha’anin kuɗi da kula da kasuwanci.
Mista Forson ya yi wa’adi biyar a majalisar dokoki kuma yana da digirin digirgir kan sha’anin hada-hadar kuɗi daga Jam’iar Kimiyya da Fasaha ta Kwame Nkrumah.
Haka kuma ya yi digirinsa na biyu kan haraji da tattalin arziƙi daga Jami’ar Oxford ta Ingila da kuma Jam’iar Kimiyya da Fasaha ta Kwame Nkrumah.
Dominic Akuritinga Ayine
Dakta Dominic Akuritinga Ayine babban lauya ne wanda ya shafe shekara talatin yana aikin lauya.
A baya ya taba zama mataimakin Atoni-Janar kuma Ministan Shari’a.
Yana da digirin digirgir a fannin shari'a daga Jami'ar Stanford, sannan yana da digiri na biyu daga Makarantar Horas da Lauyoyi ta Shari'a ta Jami'ar Michigan, da kuma digiri na lauya daga Jami'ar Ghana.
Ya kuma koyar a makarantar horas da lauyoyi ta Jami’ar Ghana tsawon shekaru.