Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya amince da dage kidayar jama’ar kasar da gidaje wadda aka yi niyyar gudanarwa daga 3 zuwa 7 ga watan Mayun 2023.
Ma’aikatar watsa labarai da al’adu ta kasar ce ta bayyana hakan a wata sanarwar da ta fitar a ranar Asabar.
Ma'aikatar ta ce bayyana cewa sabuwar gwamnatin da za ta gaji mulki za ta sanar da sabon jadawali da kuma ranakun da za a gudanar da kidayar.
A ranar Juma’a ne shugaban hukumar kidaya ta Nijeriya Honarabul Nasir Isa Kwarra ya kai ziyara ga Shugaba Muhammadu Buhari inda ya ba shi bayanai kan halin da ake ciki kan batun shirye-shiryen kidayar.
Sai dai a sanarwar da gwamnatin ta fitar, ba ta bayar da wata kwakkwarar hujja ba kan dalilin da ya sa aka dage kidayar, sai dai a kwanakin baya an ta rade-radi kan cewa akwai yiwuwar a dage kidayar saboda wasu shirye-shirye da ba a kammala ba.
Sanarwar ta ce Shugaba Buhari ya yaba kan irin tsare-tsaren da hukumar kidayar ta fito da su musamman samar da kayayyakin kimiyya wadanda za su iya gudanar da kidaya da za a yi alfahari da ita a duniya.
“Shugaban kasa ya bayar da umarni ga hukumar da ta ci gaba da shirye-shiryen kidayar jama’a da gidaje ta 2023 domin cin moriyar ci gaban da aka samu da kuma samar da wata turba da gwamnati mai zuwa za ta amfana da wadannan nasarorin,” in ji sanarwar.
An dai soma kidayar jama’a a Nijeriya shekaru biyu bayan samun ‘yancin kan kasar a 1962 inda aka kididdige cewa jama’ar kasar sun kai miliyan 45.5.
Kidaya ta karshe da aka yi a kasar an yi ta ne a 2006 inda aka kididdige cewa akwai sama da mutum miliyan 140 a kasar, sa’annan a 2019 kuma hukumar ta yi hasashen cewa jama’ar kasar sun haura mutum miliyan 200.