Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya ce marigayi Sheikh Abubakar Giro Argungu mutum ne da ba ya tsoron tsayawa don kare mutuncin talaka da kuma gaya wa shugabanni gaskiya.
Ya bayyana haka ne a wata sanarwa da kakakinsa Ajuri Ngelale ya fitar domin yin ta'aziyyar rasuwar fitaccen malamin na addinin Musulunci.
Sheikh Argungu ya rasu ne ranar Laraba a birnin Kebbi bayan ya yi fama da gajeriyar jinya.
Shugaban kasar ya ce: "Za a yi kewar Sheikh Giro bisa rashin tsoronsa a fafutukar kare talakawa da kuma gaya wa shugabanni gaskiya don su yi ayyukan da suka rataya a wuyansu."
Shugaba Bola Tinubu ya bayyana rasuwar Sheikh Giro Argungu a matsayin "rashin da ya girgiza ba wai kawai mabiyan malamin ba, har ma da kasar baki daya" saboda gudunmowarsa wajen karantar da addinin Musulunci.
"Za a dade ana tuna muryar Sheikh Giro Argungu saboda yada addinin Musulunci da tsare gaskiya. Ayyukan da Malamin ya yi ta hanyar kungiyar JIBWIS, inda ya taba rike mukamin shugaban babban kwamitin, sun yi gagarumar taimakawa wajen fahimtar da matasan Musulmai masu dimbin yawa a shekaru da dama," in ji sanarwar.
Shugaban kasar na Nijeriya ya yi ta'aziyya ga iyalai da gwamnati da kuma al'ummar jihar Kebbi bisa wannan babban rashi.