Kwamandan hukumar Hisbah ta jihar Kano da ke arewacin Nijeriya Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya sauka daga muƙaminsa.
Fitaccen malamin na addinin Musulunci ya sanar da ajiye muƙamin nasa ne ranar Juma'a da safe a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta.
Ya ɗauki matakin ne kwana guda bayan gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya caccaki hukumar ta Hisbah bisa salon ayyukanta waɗanda ya ce suna keta doka.
Sheikh Daurawa ya ce gwiwoyinsa sun yi sanyi bayan da ya saurari kalaman gwamnan kan sukar da ya yi wa hukumar Hisbah.
Sai dai a jawabin Sheikh Daurawa, ya bai wa gwamnan haƙuri sannan ya bayyana cewa ya sauka daga muƙaminsa.
"Ina bai wa mai girma gwamna (Abba Kabir Yusuf) haƙuri bisa fushi da ya yi da maganganu da ya faɗa, kuma ina roƙon ya yi min afuwa. Na sauka daga kan wannan muƙami da ya ba ni na Hisbah. Kuma ina yi masa addu'a, ina yi masa fatan alheri," in ji Malamin.
Tun da farko a ranar Alhamis, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce hukumar Hisbah ta jihar Kano tana aikata "kuskure babba" game da yadda take gudanar da wasu ayyukanta a yunƙurin yaƙi da masu aikata ɓarna.
Gwamna Abba Gida-Gida, kamar yadda aka fi saninsa, ya ce akwai kura-kurai da dama a salon da Hisbah take bi wurin kama masu aikata ɓarna musamman mata da matasa.
''An je inda wasu matasa ke ɓarna - maza da mata - amma yadda aka dinga ɗebo su ana duka da gora, suna gudu ana bin su da gora ana taɗe ƙafafunsu, ana ɗebo su kamar awaki a jefa su cikin mota (Hilux), wannan muna gani kuskure ne babba,'' a cewar gwamnan na jihar Kano.