Gwamnatin kasar Senegal ta hana amfani da shafin sada zumunta na TikTok, tana mai cewa an yi amfani da shafin na musayar bidiyo wajen ruruta wutar tashin hankalin da ta biyo bayan kama shugaban ‘yan adawa Ousmane Sonko.
Hukumomin kasar sun riga sun katse intanet tun ranar Litinin, a wani lamari da kungiyoyin kare hakkin bil Adama suka yi Allah wadai da shi, kamar yadda suka yi kan matakin haramta jam’iyyar adawa ta Sonko.
A cewar Ministan Sadarwar kasar, Moussa Bocar Thiam a ranar Laraba, "Manhajar TikTok ita ce manhajar sada zumunta da aka fi amfani da ita wajen watsa sakonnin kiyayya, da na yi wa gwamnati zagon-kasa. Wannan lamarin yana barazana ga zaman lafiyar kasa."
An samu tashin hankali bayan an gurfanar da Ousmane Sonko a gaban kotu ranar Litinin kan zargin tayar da zaune-tsaye da alaka da kungiyar ta’adda, da kuma wasu laifuka.
Akalla mutum uku sun mutu a tashin hankalin, yayin da wasu mutum biyu suka mutu a wani harin bam din fetur, da aka kai kan wata motar bas a wajen babban birnin kasar Dakar.
Kawo yanzu, ba a tabbatar da alaka tsakanin zanga-zangar da harin bas din ba.