Ana zargin tsare Seaman Abbas Haruna ba bisa ƙa'ida ba tsawon shekara shida. / Hoto: DHQ

Hedikwatar Tsaron Nijeriya ta bayar da umarni kan a ƙaddamar da bincike dangane da tsare sojan ruwan nan na Nijeriya Seaman Abbas Haruna, kamar yadda sanarwar da ta fitar ta bayyana.

A ƙarshen makon da ya gabata ne aka ga wani bidiyo na yawo a kafofin sada zumunta inda aka ga matar Seaman Abbas tana zargin wani babban soja da tsare mijinta tsawon shekaru shida.

“Hedikwatar Tsaron Nijeriya ta kula da wani bidiyo wanda ke yawo kan tsare wani sojan ruwa Seaman Abbas Haruna tsawon shekara shida.

“Hedikwatar Tsaron Nijeriya na son bayar da tabbaci ga jama’a kan cewa sojojin Nijeriya za su ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da adalci, gaskiya, da bin doka da oda. Tsarin kotun soja duk da cewa ana takatsantsan, ana tabbatar da adalci da ba kowa dama bisa ka'idojin aikin soja da doka,” in ji sanarwar.

Haka kuma sanarwar ta ƙara da cewa tuni babban hafsan tsaron ƙasar Janar Christopher Musa ya bayar da umarni kan gudanar da bincike kan lamarin, da kuma bayyana sakamakon binciken ga jama’a.

TRT Afrika