Gwamnatin Malawi ta ayyana kwanaki 21 na makoki a fadin ƙasar don girmama mataimakin shugaban ƙasar Saulos Chilima da wasu mutane takwas da suka mutu a hatsarin jirgin sama.
Da safiyar ranar Litinin ne jirgin sojin da ya ɗauko mataimakin shugaban ƙasar da tawagarsa ya yi ɓatan-dabo, bayan da ya gaza sauka saboda rashin kyawun yanayi.
Jirgin ya tashi ne daga babban birnin ƙasar Lilongwe zuwa Mzuzu wanda ke da tazarar kilomita 230, inda za a yi jana’izar wani tsohon ministan ƙasar.
An tsinci sauran tarkacen jirgin ne a ranar Talata a cikin wani babban daji mai tsaunuka da ke kusa da garin Mzuzu.
An soma makoki na ƙasa baƙi ɗaya ne daga ranar Talata 11 ga watan Yuni zuwa ranar Litinin 1 ga watan Yuli, kamar yadda majalisar ministocin ta bayyana a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Talata.
Yin ƙasa da tutar ƙasar
Shugaban ƙasar Lazarus Chakwera ya ba da umarni a yi ƙasa-ƙasa da tutar ƙasar a ko ina a fadin ƙasar har tsawon lokacin makokin.
Majalisar ministocin ƙasar ta ce daga baya za a fitar da cikakken bayani game da lokacin da za a yi jana'izar waɗanda suka mutu a hatsarin.
An kai gawar Chilima da 'yan tawagarsa da suka mutu zuwa babban birnin ƙasar Lilongwe.
Shugaba Chakwera ya samu rakiyar ministocin gwamnati da wasu jami'ai domin karɓar gawawwakin a filin jirgin saman Kamuzu a yammacin ranar Talata.
Manyan shugabannin duniya sun yi ta miƙa saƙon ta'aziyyarsu ga iyalai da kuma gwamnatin ƙasar ta Malawi.