Sai dai sanarwar ta ambato Kwamishinan 'yan sanda na Jihar Mohammed Usaini Gumel yana mai tabbatar da cewa sun ɗauki dukkan matakan tsaro da za su bai wa Alhaji Aminu Ado Bayero domin ya yi Sallar Juma'a a masallacin da ke Fadar Sarki ta Nasarawa inda yake zaune. / Hoto: Others

Rundunar 'yan sandan Nijeriya reshen jihar Kano ta ƙaryata rahotannin da ke cewa Sarkin Kano na 15 Alhaji Aminu Ado Bayero zai jagoranci Sallar Juma'a a Masallacin Kofar Kudu da ke cikin Birni.

Ta bayyana haka ne a wata sanarwa da kakakin Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar ranar Juma'a da safe.

"Rundunar 'yan sanda reshen Jihar Kano tana mai umartar dukkan mutane su yi watsi da labaran ƙarya da ake watsawa a soshiyal midiya cewa Sarki Alhaji Aminu Ado Bayero zai jagoranci Sallar Jumma’t a Babban Masallaci da ke Ƙofar Kudu, Kano," in ji sanarwar.

Sai dai sanarwar ta ambato Kwamishinan 'yan sanda na Jihar Mohammed Usaini Gumel yana mai tabbatar da cewa sun ɗauki dukkan matakan tsaro da za su bai wa Alhaji Aminu Ado Bayero domin ya yi Sallar Juma'a a masallacin da ke Fadar Sarki ta Nasarawa inda yake zaune.

Kazalika Kwamishinan ya tabbatar da cewa 'yan sanda da dukkan sauran jami'an tsaro za su bayar da cikakken tsaro a Fadar Sarki Muhammadu Sanusi II inda ake sa rai zai gudanar da Sallar Juma'a.

TRT Afrika