Mutane na tserewa bayan an samu fashe-fashe a unguwar Embakasi dake Nairobi ranar biyu ga watan Fabrairu 2, 2024. / Hoto: AFP

'Yan majalisar dattawan Kenya sun gayyaci jami'an hukumar da ke sanya ido kan harkokin makamashi da man fetur na kasar (Epra), ciki har da shugabansu, bayan gobara ta tashi a wata cibiyar sayar da gas na girki a Nairobi.

Lamarin ya faru ne ranar Alhamis da tsakar dare, a cewar ganau.

Akalla mutum uku sun mutu kuma mutum 300 sun jikkata sakamakon gobarar, kamar yadda kungiyar bayar da agaji ta Red Cross ta Kenya da kuma jami'ai suka bayyana.

Ana fargabar cewa za a iya samun karin mace-mace.

Wani dan majalisar dattawa da ke wakiltar Nairobi Edwin Sifuna ya shaida wa jaridar Kenya’s Standard cewa gayyatar ta zama wajibi domin jami'an su yi "bayani game da inda dukkan cibiyoyin sayar da iskar gas na girki masu rajista suke da kuma matakan da aka dauka na tabbatar da tsaron lafiyar mutane a inda suke."

Kungiyar ba da agaji ta Red Cross a Kenya ta bayyana ranar Juma'a a shafinta na X cewa "ma'aikatan bayar da agajin gaggawa daban-daban sun kubutar da mutum 271 inda aka kai su cibiyoyoin kiwon lafiya da ke Nairobi."

Ta kara da cewa an yi wa mutum 27 magani nan-take a wurin da lamarin ya faru.

Bidiyoyin da aka dauka a unguwar Embakasi sun nuna 'yan kwana-kwana suna kokarin kashe gobarar.

Wani mai magana da yawun gwamnati ya bayyana cewa ana kokarin cika tukwanen iskar gas ne a lokacin da gobarar ta tashi da misalin karfe sha biyu na dare ranar Alhamis.

Ganau sun bayyana wa kafafen watsa labarai na kasar cewa sun ji mostin kasa bayan fashewar.

TRT Afrika