'Yan majalisar dattawa na arewacin Nijeriya sun nuna adawarsu da yunkurin kungiyar raya tattalin arzikin kasashen Yammacin Afirka, ECOWAS, na yin amfani da karfin soji a kan sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar.
Sun bayyana haka ne ranar Juma'a a yayin da shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya rubuta wasika ga majalisar dattawan kasar yana neman amincewarta don daukar matakin soji kan dakarun da suka kifar da gwamnatin Mohamed Bazoum a makon jiya.
Shugaban ya kuma nemi izinin daukar wasu matakai ciki har da katse wutar lantarkin da Nijeriya ke bai wa Nijar.
Shugaban majalisar dattawan kasar Godswill Akpabio ne ya karanta wasikar da Shugaba Tinubu ya rubuta wa majalisar a zaman da ta yi ranar Juma’a.
Ya aike da wasikar ne bayan rashin nasarar tawagar da kungiyar ECOWAS ta tura Nijar don tattaunawa da sojojin kasar don mayar da Shugaba Bazoum kan mulki.
An yi amannar cewa ana tsare da Bazoum a fadar shugaban kasa.
Abin da ya shafi Nijar zai shafi Nijeriya
Sai dai a taron da 'yan majalisar dattawan na arewacin Nijeriya suka yi sun ce ya kamata a yi hattara game da yunkurin tura sojoji Jamhuriyar Nijar.
Sanata Abdulrahman Kawu Sumaila, kakakin 'yan majalisar dattawan arewacin Nijeriya, ya bukaci kungiyar ECOWAS ta ci gaba da tattaunawa da sojojin da suka kifar da gwamnatin Bazoum har a gano bakin zaren.
Ya ce alakar arewacin Nijeriya da Jamhuriyar Nijar dadaddiya ce da bai kamata a rusa ta ta hanyar shigar da sojojin ECOWAS kasar ba.
Sun kara da cewa Jamhuriyar Nijar ta bai wa 'yan gudun hijirar Nijeriya mafaka yayin yakin Boko Haram kuma yanzu haka dubban 'yan Nijeriya ne ke ci gaba da samun wurin zama a Nijar.
A cewarsu, duk wani abu da zai haifar da yaki da Nijar zai sa arewacin Nijeriya ta hargitse.
"Jihohin arewacin Nijeriya bakwai ne ke da iyaka da Jamhuriyar Nijar" don haka tura mata sojoji zai dagula lamura a yankin, a cewar Sanata Sumaila.
Su ma wasu malaman addini na yankin arewacin Nijeriya sun yi gargadi game da daukar matakin soja kan Nijar.
Yanke hulda
Sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar sun yanke alaka ta diflomasiyya da Nijeriya da Togo da Amurka da kuma Faransa.
Nijeriya ta katse wutar da take bai wa Nijar, lamarin da ya jefa wasu bangarorin kasar cikin duhu.
Nijar na sayen kashi 70 cikin 100 na wutar lantarkinta daga kamfanin wutar lantarkin Nijeriya.
Ranar Alhamis, tawagar da Shugaba Tinubu ya tura Nijar ba ta samu ganin shugaban sojojin da suka yi juyin mulki da kuma hambararren Shugaba Mohammed Bazoum ba.
Tsohon Shugaban Nijeriya Abdulsalami Abubakar ne ya jagoranci tawagar.
Nijeriya, kasa mafi yawan al'umma a Afirka, ita ce ke rike da shugabancin Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Afirka Ta Yamma (ECOWAS), wadda ta kakaba takunkumi kan kasar ranar Lahadi.
Sai dai kuma Shugaba Bola Tinubu, ya ce kungiyar ECOWAS za ta yi iya kokarinta na ganin cewar an sasanta rikicin cikin lumana, amma kungiyar za ta iya daukar matakin soji a karshe idan sauran matakai suka ci tura.
Jagororin juyin mulkin Nijar sun yi gargadin cewar za su mayar da martani mai karfi kan duk wani matakin sojin da aka dauka a kansu.