Jiigin wanda aka kama yana ɗauke ne da mutum huɗu. / Hoto: SLCAA

An kama wani jirgin sama mai zaman kansa a Freetown babban birnin Saliyo inda hukumomi a ƙasar ke gudanar da bincike bayan jirgin ya sauka ba tare da ba shi izini ba.

Jirigin ya taso ne tun daga Liberia inda yake hanyarsa ta zuwa ƙasar Mexico sai ya sauka ba tare da izini ba a filin jirgin ƙasa da ƙasa na Freetown da ke Saliyo, kamar yadda ma'aikatar watsa labarai ta ƙasar ta bayyana.

Jirgin saman wanda ke iya ɗaukar mutum 14, yana ɗauke ne da mutum huɗu har da matuƙin jirgin, haka kuma jirgin na da lambar rajista ta bogi, inda wasu sassa na lambar rajistar ma sun goge, kamar yadda ma'aikatar ta bayyana a sanarwar da ta fitar.

Haka kuma sanarwar ta tabbatar da cewa mutum uku a cikin jirgin an same su da fasfon Mexico sai kuma mutum ɗaya na ɗauke da fasfon Sifaniya.

'Babu abin tuhuma'

"Bayan binciken da 'yan sanda suka yi, 'yan sandan ba su ga wani abin tuhuma ba a cikin jirgin. Yanzu haka an mika dukkan mutum hudun da aka samu a cikin jirgin ga 'yan sandan Saliyo don ci gaba da bincike," in ji sanarwar.

Hukumomin kasar sun ce jirgin bai tashi daga wani sanannen filin jirgin sama ba a Laberiya kuma ba shi da izinin sauka.

Matuƙin jirgin ya sauka da jirgin ba tare da tuntuɓar masu kula da zirga-zirgar jiragen sama ba haka kuma tuni aka soma bincike kan masu kula da zirga-zirgar jiragen sama biyu, kamar yadda sanarwar ta ƙara da cewa.

"Waɗanda ke cikin jirgin sun yi iƙirarin sun samu matsala da na'urar sadarwarsu kafin su sauka, sai dai wani bincike da aka gudanar an gano na'urar na aiki," in ji ta.

TRT Afrika