Shugaban jam'iyyar uMkhonto weSizwe (MK)  da tsohon shugaban Afirka ta Jacob Zuma (Dama) da kakakin jam'iyyar MK Nhlamulo Ndhlela (Hagu) da kuma babban lauyanta Dali Mpofna cikin mahalarta taron manema labarai da suka gudanar a Johannesburg ranar 16 ga watan Yunin 2024, kwana biyu bayan sake zaɓen Cyril Ramaphosa a matsayin shugaban ƙasar./ Hoto: AFP

Tsohon shugaban Afirka ta Kudu Jacob Zuma ya ce sabuwar jam'iyyarsa ta uMkhonto weSizwe (MK) za ta shiga ƙawancen jam'iyyun adawa domin bijire wa gwamnatin ƙasar, yayin da take ci gaba da ƙalubalantar sakamakon zaɓen da aka gudanar.

Jam'iyyar MK ta ce za ta shiga sabon ƙawance na 'yan majalisar dokokin jam'iyyun hamayya wanda ya ƙunshi galibin jam'iyyu masu son kawo sauyi.

Ƙawancen wanda ake kira "Progressive Caucus" a Turancin Ingilishi yanzu haka jam'iyyar Economic Freedom Fighters (EFF), wadda ta lashe kujeru 39 na 'yan majalisar dokoki, ita ce take jagorantarsa.

Duk da "fashi da makamin da aka yi da rana tsaka" na ƙuri'u, jam'iyyun da ke cikin wannan gamayya sun samu kusan "kashi 30 na kujerun 'yan majalisar dokoki," in ji kakakin jam'iyyar uMkhonto weSizwe (MK) Nhlamulo Ndhlela

Ya ce hakan ya "ba mu damar kasancewa 'yan hamayya masu ƙarfi waɗanda za su yi yaƙi domin ƙwato tattalin arzikin baƙake da kuma al'ummar Afirka."

A taron manema labaran da suka gudanar, Ndhlela ya yi jawabi ne a madadin tsohon shugaban ƙasar mai shekara 82. Zuma, wanda ya ci-magani a yayin taron, bai ce komai ba lokacin da ake karanta takardar taron, ko da yake lokaci zuwa lokaci ya amsa tambayoyi daga 'yan jarida.

"An murɗe zaɓukan 2024," in ji Ndhlela. "Mun umarci tawagar lauyoyinmu ta ɗauki dukkan matakan da suka dace a Afirka ta Kudu da ma ƙasashen duniya domin tabbatar da ganin an yi adalci."

Ya ƙara da cewa, "Idan lokaci ya yi za mu yi kira ga mutanenmu su yi zanga-zangar lumana a kan tituna da kotuna da kuma majalisar dokoki don nuna don nuna rashin gamsuwarsu kan wannan rashin adalci sannan su dage har sai an yi abin da ya dace."

Jam'iyyar MK ta zo ta uku a zaɓen inda ta samu kashi 14.6 na ƙuri'un da aka kaɗa da kuma kujeru 58 na majalisar dokoki.

TRT Afrika da abokan hulda