Ma’aikatar lafiya ta Ghana ta tabbatar da bullar sabon nau’in sauro mai suna ‘Anopheles stephensi’ a kasar.
A wata sanarwa da ma’aikatar lafiya ta kasar ta wallafa a shafinta na Facebook a ranar Lahadi, ta ce an soma tabbatar da sabon nau’in ne a watan Maris, bayan an dauki samfarin gwaji daga garuruwan Tuna da Dansoman da ke yankin Greater Accra.
Ma’aikatar lafiyar ta ce an dauki wannan gwajin ne a matakin da ake dauka na sa ido kan sauro da cutar Maleriya a fadin kasar.
Sabon nau’in sauron ya bulla ne kwanaki kadan bayan Ghana ta zama kasa ta farko a duniya da ta amince a soma amfani da rigakafin maleriya na R21 wanda aka dade ana jira.
Tun a 2019 ne dai Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta yi gargadi kan sabon nau’in na sauron wanda ta ce ya shiga nahiyar Afirka.
Wannan nau’in na sauro zai iya hayayyafa a wurare da dama da suka hada da kududdufai da fadamu da cikin tankunan ruwa da duk wani wuri da ruwa zai iya kwanciya.
Saannan bayanai sun tabbatar da cewa irin wannan sauron zai iya rayuwa a yankuna da ke da akwai tsananin zafi.
Haka kuma sauron zai iya sabawa da yanayi daban-daban cikin sauri wanda hakan zai kawo cikas wurin kawar da shi.
Sauro ne ke haddasa cutar maleriya wadda aka yi kiyasin cewa tana kashe yaro guda a duk minti daya a kullum a fadin duniya.
Kungiyar agajin rigakafi ta Vaccine Alliance ta tabbatar da cewa a shekarar 2021 a kasar Ghana kadai, an samu mutum miliyan 5.3 da suka kamu da cutar maleriya sa’annan cutar ta kashe mutum 12,500.