Shugaban kasar Saliyo Julius Bio ya yi umarnin a gudanar da cikakken bincike game da rushewar wani gini mai hawa bakwai a babban birnin ƙasar da ya yi ajalin akalla mutane takwas da suka hada da yara kanana uku, yayin da wasu suke karkashin ginin.
Ginin da ke gabashin Freetwon, da ake amfani da shi a matsayin gidaje da wuraren aiki, ya ruguje a ranar Litinin, in ji Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Kasa a wata sanarwa da ta fitar.
Wadanda suka mutu sun hada da maza manya uku, mata manya biyu, yara mata biyu 'yan kasa da shekaru biyar da yaro karami dan kasa da shekaru biyar
"Za mu gudanar da cikakken bincike kan wannan ibtila'i, sannan mu yi duk mai yiwuwa don hana afkuwar irin wannan a nan gaba." in ji shugaba Bio a wani sako ta shafin X.
Aikin ceto
Har yanzu ba a san musabbabin rushewar ginin ba, amma an ce akwai mutane da dama da ke rayuwa a cikinsa.
Ana gudanar da aikin ceto da kugiyoyi manya inda shugaban kasa ya bayyana cikakken goyon baya ga Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Kasa.
"Za mu yi duk kokari wajen ceto mutane, sannan mu taimaka wa wadanda suka tsira da rayukansu."
Wani dan jaridar AFP ya ga masu aikin ceto na amfani da hannayensu da tebura da gatari don neman wadanda ke karkashin ginin.
Gano wadanda lamarin ya rutsa da su
Dandazon jama'a na ci gaba da taruwa a gaban ginin da ya rushe, suna ta kokarin ganin an kubutar da mutanen.
Hukumar Bayar da Agajin Gaggawar ta kuma ce suna "ci gaba da aikin ceto, suna fatan gano mutanen da ke karkashin ginin da ya rushe."
Hukumar ta kara da cewa "Suna ci gaba da auna irin asarar da aka yi don taimakawa wajen hana rushewar gine-gine a kasar."