Rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta musanta zargin ɓacewar makamai 3, 907 daga hannunta, tana mai cewa zargin ba shi da tushe bare makama.
Wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, Olumuyiwa Adejobi, ya fitar ta ce da alama wannan zargin ya samo asali ne daga wani binciken da ofishin babban mai binciken kuɗi na ƙasa ya yi tun shekarar 2019 kafin sufeto janar na ‘yan sanda mai ci yanzu ya kama aiki.
Sanarwar ta ce rahoton dai ya nuna cewa makamai 3,907 ne ba a bayar da bayanin yadda aka yi da su ba, maimakon yadda aka yi ta yayatawa cewa sun ɓata .
Wannan na zuwa ne bayan wani kwamiti na majalisar dattawan Nijeriya ya buƙaci jin bahasi game da ɓacewar makamai 3,907 a ƙasar.
“Zuwa watan Disambar 2018, ba a ga jimillar bindigogi 178,459 ba, ciki har da bindigogin AK-47 88,078. Bugu da kari, zuwa watan Janairun 2020, akalla bindigogi 3,907 sun bata,” in ji rahoton.
Sai dai kuma sanarwar da rundunar ‘yan sandan ƙasar ta fitar ta ce ba lallai ba ne a samu dukkan makaman rundunar a ƙasa a lokacin da masu bincike suka ziyarci ofisoshin ‘yan sanda domin akan bai wa ‘yan sanda makamai domin fita aiki, kuma ayyukan kan iya kaiwa na tsawon watannin.
“Yana da muhimmanci a fahimci ƙalubalen da ‘yan sanda ke fuskanta a lokacin da ake tashin hankali, a lokacin da aka kashe ‘yan sanda kuma aka yi awon gaba da makamansu,” in ji sanarwar da Adejobi ya fitar.
“Duk da haka, mun yi iya ƙoƙarinmu domin mu samo bayanai game da dukkanin makaman da aka ɗauka kuma an ƙwato da yawa daga cikinsu a halin yanzu," in ji sanarwar.
A dai watan Oktoban shekarar 2020 dai an samu tashin hankali sakamakon zanga-zangar EndSARS inda aka kashe wasu ‘yan sanda kuma aka yi awon gaba da makamansu a birnin legas.