Babban sufeton 'yan sandan Nijeriya ya sha alwashin magance matsalar garkuwa da mutane a fadin kasar. Hoto/NPF

Rundunar 'yan sandan Nijeriya ta ce dakarunta sun ceto akalla mutum 154 daga hannun masu garkuwa da mutane a mako biyu da suka gabata.

Rundunar ta bayyana haka ne a wata sanarwa da kakakinta Olumuyiwa Adejobi ya fitar ranar Juma'a da maraice wadda kuma aka wallafa a shafukan intanet na rundunar.

Kazalika rundunar ta ce ta kama mutum 139 da ake zargi da hannu a satar jama'a a sassa daban-daban na kasar tare da kwace tarin makamai.

"Daya daga cikin manyan nasarorin da muka samu ita ce kama wani gungun mutane a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna wadanda su ne manyan masu kai makamai ga 'yan bindigar da suka addabi jihohin Neja da Zamfara da Kaduna," a cewar sanarwar.

A baya-bayan nan, rundunar ta ce ta matsa kaimi wajen murkushe matsalar masu garkuwa da mutane musamman a jihohin arewa maso yammacin Nijeriya da ma babban birnin kasar Abuja.

A makon jiya rundunar 'yan sandan Nijeriya ta ce jami'an tsaro sun kubutar da 'yan matan nan biyar da ke hannun masu garkuwa da mutane bayan 'yan bindiga sun kashe 'yar'uwarsu wato Nabeeha Al-Kadriyar, ko da yake lamarin ya haifar da ce-ce-ku-ce bayan danginsu sun ce sai da suka biya kudin fansa aka sake su.

Haka kuma rundunar 'yan sandan Nijeriya ta Abuja ta ce ta yi nasarar kama wani da ake zargin gawurtaccen mai yin garkuwa da mutane ne a babban birnin kasar mai suna Chinaza Phillip.

TRT Afrika