| Hausa
AFIRKA
2 MINTI KARATU
Rundunar 'yan sanda a Abuja ta karyata labarin tashin bam a Maitama
Rundunar 'yan sanda a babban birnin tarayyar Nijeriya Abuja ta karyata  fashewar wani abu da aka ji a unguwar Maitama, tana mai cewa ba bam ba ne wata kwantenar shara ce ta karfe da ta dauki zafi sai ta yi bindiga ta kama da wuta.
Rundunar 'yan sanda a Abuja ta karyata labarin tashin bam a Maitama
Rundunar 'yan sanda a Abuja ta karyata labarin tashin Bam a Maitama . / Hoto: Getty / Others
24 Janairu 2024

Rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Nijeriyya Abuja ta karyata rahoton fashewar wani bam a Maitama a yau Laraba.

A binciken da rundunar ta gudanar ta gano cewa wata kwantenar karfe ta shara ce ta dauki zafi kana ta kama da wuta, lamarin da ya yi sanadiyar jikkatar wasu masu kwashe shara biyu, wadanda a halin yanzu suke asibitin Maitama suna samun kulawar likitoci.

A sanarwar da rundunar 'yan sanda ta fitar da ke dauke da sa hannun mai magana da yawunta Josephine Adeh ta ce '' tuni aka tura tawagar masu ba da agajin gaggawa da kuma sashen kawar da ababen fashewa don tantance lamarin.''

''Lamarin ya auku ne a ranar 24 ga watan Janairu da misalin karfe 11:45, kusa da wata bola a wajen harabar Ofishin Bureau of Public Enterprise da ke Maitama a Abuja ba bam ba ne,'' a cewar sanarwar.

Rundunar ta bukaci al'umma su yi taka-tsan-tsan tare da kiyaye amfani da kwantenar shara ta karfe, a maimakon hakan ta ba da shawarar a dinga amfani da roba don zuba shara, don rage hatsarin zafin da karfe ke dauka.