Shugaban Sojojin Nijeriya Christopher Musa ya bayar da umarni a gudanar da cikakken bincike kan mutuwar sojojin. / Hoto:AP

Hedkwatar Tsaron Nijeriya ta ce ta ƙaddamar da gagarumin bincike bayan wasu matasa sun kashe sojojinta aƙalla goma sha shida a Jihar Delta da ke kudu maso kudancin ƙasar.

Daraktan watsa labarai na sojin ƙasar Birgediya Janar Tukur Gusau ne ya tabbatar da kisan sojojin a wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar

Ya ce sojojin sun rasu ne a yayin da suka kai ɗauki wurin da ake wani rikicin ƙabilanci a Ƙaramar Hukumar Bomadi ta Jihar Delta.

Rundunar tsaron Nijeriyar ta tabbatar da cewa an kashe kwamanda ɗaya da sojoji biyu masu muƙamin manjo da kyaftin ɗaya da kuma kuratan sojoji 12.

Birgediya Janar Tukur Gusau ya ce sojojin sun rasu a lokacin da suka yi ƙokarin kwantar da wata tarzoma da ta ɓarke tsakanin ƴan ƙabilar Okuama da Okoloba a ranar Alhamis.

"Wasu matasa ne suka kewaye sojojin ranar Alhamis 14 ga watan Maris sannan suka kashe su," in ji kakakin hedkwatar tsaron ta Nijeriya.

Sanarwar ta ce Shugaban Sojojin Nijeriya Christopher Musa ya bayar da umarni a gudanar da cikakken bincike kan mutuwar sojojin.

TRT Afrika