Duk da cewa rundunar sojin kasar ba ta fadi dalilin sayar da jirgin ba, amma ta fadi matakan da masu sha’awa za su bi don saye./Hoto: Rundunar Sojin Saman Nijeriya

Rundunar sojin Nijeriya ta ce za ta yi gwanjon jirgin samanta bisa amincewar gwamnatin tarayyar kasar.

Wannan lamari na zuwa ne a ranar da rundunar sojin kasar ta dauki alhakin kai harin sama bisa kuskure kan wani taron masu Maulidi a wani kauye a Jihar Kaduna da ke arewacin kasar.

“A bisa tanade-tanaden dokar sayen kaya ta shekarar 2007, rundunar ta NAF tana gayyatar duk masu sha'awa da su gabatar da tayin sayen jirgin,” a cewar sanarwar da rundunar sojin saman kasar ta wallafa a shafinta na Facebook ranar Litinin da daddare, mai dauke da sa hannun Daraktan Watsa Labarai, Air Commodore EK Gabkwet.

NAF ta kara da cewa masu sha’awar sayen jirgin kirar Falcon 900 mallakin rundunar sojin saman kasar za su iya aika sako ta imel ko su je ofishinta kai-tsaye.

Matakan nuna sha’awar saya

Duk da cewa rundunar sojin kasar ba ta fadi dalilin sayar da jirgin ba, amma ta fadi matakan da masu sha’awa za su bi don saye kamar haka:

Idan ta imel za a tura sha’awar saya, dole a sanya lambobin sirrin da aka rufe sai a aika adireshin dproc@airforce.mil.ng, yayin da ita kuma lambar sirrin za a aika ta wani adireshin imel din na daban na dproc2@airforce.mil.ng.

Idan kuma kai tsaye mai son saye zai kai,to sai a sanya takardar bayyana sha;awar sayen kunshe a cikin ambulan a like, tare da sanyta suna da adireshin kamfani ko mai son saya da kuma rubuta bukatar hakan a bayan ambulan din.

Kazalika za a rubuta baro-baro da manyan baki cewa ‘KAR A BUDE HAR SAI RANAR 24 DA DISAMBAN 2023’.

Idan kuma aika takardar nuna son sayen za a yi ta hanyar amfani da masu kai sako, to a tabbatar kai tsaye an mika ta ga sashen kula da kayayyakin rundunar da ba da kwangila a hedikwatar NAF da ke Abuja, dauke da adireshin zuwa ga Hafsan Rundunar Sojin Sama.

NAF ta ci gaba da cewa za a fara tantance bukatun wadanda suka nuna sha’awa da zarar ranar da aka sanya ta karewar wa’adin shigar da bukatar ta kare.

Kazalika ba za a kula wanda ya aika bayan kurewar lokaci ba ko kuma wanda bai aika lambobin sirri ba.

Ta ce jirgin yana nan a wajen ajiyar jirage mai lamba 307 EAG a babban filin jirgin sama na kasa da kasa na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja, babban birnin Nijeriya, “kuma duk mai son sha’awar saye da ke son ganinsa yana iya zuwa daga ranar 1 zuwa 24 ga watan Disamban 2023.

NAF ta bayyana wasu muhimman bayanai kan jirgin kamar haka:

  • An fara amfani da jirgin ne ranar 3 ga watan Oktoban 1990
  • Yana da girman daukar fasinja 16 da ma’aikata uku
  • Ya yi aiki na tsawon sa’a 12,094:35 tun fara amfani da shi.

TRT Afrika