Rundunar soji ta nemi ‘yan Nijeriya da su yi watsi da rahoton wanda ta ce an ƙirƙire shi ne ba tare da sanin dokokin aikinta ba. Hoto: NA

Rundunar Sojin Nijeriya ta ƙaryata wani rahoto da ake yaɗawa a shafukan intanet wanda ke cewa tana ɗaukar masu ikirarin jihadi aiki a ƙasar.

Sanarwar da rundunar sojin ta fitar a ranar Talata ta ce “ana yaɗa rahoton ne mai murya da ake iya jiyo muryar ƙarya ta wani jami’i yana kira ga Musulmai matasa da su shiga rundunar sojin ƙasar don yaɗa da’awar Musulunci.”

“Duba da irin mummunan tasirin da wannan ƙaryar za ta iya yi a ƙasar, rundunar soji tana shaida wa jama’a cewa wannan rahoto ba shi da alaƙa da aƙidu da muradunta.”

“An ƙirƙiri labarin ne kawai don a saka tsoro da fargaba da jawo rashin rashin aminci a tsakanin ma’aikatanmu da kuma jawo rashin aminci tsakanin al’ummomin Musulmai da Kiristoci, waɗanda ka iya jin cewa rayuwarsu da imaninsu na cikin barazana a ƙasar,” a cewar sanarwar rundunar.

Rundunar soji ta nemi ‘yan Nijeriya da su yi watsi da rahoton wanda ta ce an ƙirƙire shi ne ba tare da sanin dokokin aikinta ba. Sannan ta jaddada aniyarta ta ci gaba da kare rayukan ‘yan Nijeriya da bin dokokin aikinta ka’in da na’in.

TRT Afrika