Rundunar sojin Nijeriya ta kawar da 'yan ta'adda 10,937 ta ceto mutum 7,063 da aka sace a 2024

Hedkwatar Tsaron Nijeriya ta ce hadakar ayyukan sojojin kasa da na ruwa da na sama wadanda ke yaƙi da matsalar rashin tsaro a kasar, sun kashe jimillar 'yan ta'adda 10,937, tare da kama wasu 12,538 da kuma ceto mutum 7,063 da aka yi garkuwa da su duk a cikin shekarar 2024.

Hedkwatar Tsaron wacce ta sanar da hakan a ranar Talata, 31 ga watan Disamban 2024, ta yi nuni da cewa, jerin farmakan da aka kai tun daga watan Janairu zuwa yau, sun yi sanadin da dakaru suka rage ƙarfin ‘yan ta’adda sosai da sosai.

Daraktan yada labarai na Rundunar Tsaron, Manjo Janar Edward Buba a lokacin da yake bayyana hakan, ya ce, “A tsawon wannan shekara, sojoji sun kawar da fitattun shugabannin ‘yan ta’adda da kwamandoji da mayaƙansu fiye da dubu.

“Sojoji sun musanta satar man da aka kiyasta kudinsa ya kai dala biliyan 68 (N68,453,376,040.00).

"Sojojin sun kuma lalata haramtattun wuraren tace man fetur guda 2,612 da kwale-kwale na katako guda 2,019 da ake amfani da su wajen fasa bututan mai.

"Sojojin sun kwato lita 56,223,002 na danyen mai da aka sata, lita 9,735,836 na tattacen mai ba bisa ka'ida ba da lita 95,595 na kanazir lita 156,527 na dizal da dai sauransu.

Manjo Janar Buba ya ce a yayin artabu da suka yi, sojojin sun ƙwato makamai 8,815, alburusai 228,004 da suka hada da bindigogi kirar AK-47 guda 4,332, da bindigogi ƙirar gida guda 1,244, da bindigogi samfurin dane 838, da bindigogin samfurin action guns 259 da harsasai 128,474, da sauran makamai.

Da yake karin haske game da ayyukan, Manjo Janar ya ce, “Dakarun Operation Hadarin Daji a yankin Arewa maso Yamma, a cikin wannan shekara sun yi nasarar kashe ‘yan ta’adda 2,906, sun kama mutum 1,826 da ake zargi da kuma kubutar da mutum 2,616 da aka yi garkuwa da su.

“Bugu da ƙari, sojojin sun ƙwato bindigogi kirar AK-47 guda 1,450, da kananan bindigogi 477 da makamai iri-iri 576, da jigidar harsasai 31,999 da alburusai kuma 6,564.

“Rundunar Operation Hadarin Daji ta ci gaba da ayyukanta a duk tsawon wannan shekara domin samar da ingantaccen tsaro da kwanciyar hankali don ayyukan noma da zamantakewar al’umma a jihohin Kaduna, Katsina, Kebbi, Sokoto da Zamfara da kuma Jihar Neja.

Ayyukan sojoji sun haifar da arangama tsakanin kungiyoyin 'yan ta'adda da ya yi sanadiyar mutuwar kwamandojin 'yan ta'adda da dama a fafatawar da kungiyoyin da ke gaba da juna suka yi.

“Haka zalika, hadin gwiwa tsakanin jami’an tsaro da hukumomin leken asiri ya kara samar da nasarar kashe wasu shugabannin ‘yan ta’adda da suka hada da: Isiya Boderi, Alhaji Mubale, Baban Yara, Alhaji Kabiru, Lawali Gudau aka Damina, Buhari Alhaji Halidu aka Buharin Yadi, Nagala Jabbi, Audu Kalwa, Muhammad Sani aka Peter, Dan Hajiya, Ga'aye, Akwanga, Bala Gurgu, Yellow, Kucheri da Babban Mutum.

“Dakarun Operation Whirl Stroke sun kashe ‘yan ta’adda 600, sun kama mutum 1,006 da ake zargi da kuma ceto mutum 688 da aka yi garkuwa da su.

"Sojojin sun kuma kwato bindigogi kirar AK-47 guda 295, da sauran muggan makamai iri-iri 315, da alburusai 13,055 na musamman na NATO da sauran su.

TRT Afrika